Gwamnatin Katsina ta sauya matsayin garinsu shugaba Buhari daga 'Kauye' zuwa 'Gunduma'
- Gwamnatin jihar Katsina ta daukaka darajar kauyen Shugaba Muhammadu Buhari zuwa gudunma
- Hakan ya kasance ne a taron gaggawa da majalisar dokokin jihar ta kira a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli
- Gwamna Aminu Bello Masari ne ya gabatar da bukatar a gaban majalisar jihar
Majalisar Dokokin jihar Katsina ta amince da daukaka garin Dumurkul, kauyen Shugaba Muhammadu Buhari zuwa gudunma a masarautar Daura, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majalisar ta tafi hutu saboda bikin babban Sallah a ranar Laraba, 14 ga watan Yuli, 2021.
Ta sanya dawowa a ranar Litinin, 2 ga watan Satumba, 2021, don ci gaba da ayyukan majalisa.
Sai dai kuma, a ranar Litinin, Shugaban Majalisar, Tasi’u Musa Maigari, ya kira taron gaggawa don duba bukatar da Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari ya gabatar, na neman amincewa da tabbatar da sabuwar gundumar da aka kirkira a Masarautar Daura.
An fitar da gundumar Dumurkul daga Gundumar Koza da ke cikin Karamar Hukumar Maiadua, kamar yadda Gwamna ya amince da ita bayan bukatar hakan ta taso, kamar yadda sashi na 7 (1) (2) na Dokar Karamar Hukumar (2000) ya tanada.
Shugaban masu rinjaye na majalisar jihar, Hon. Abubakar Suleiman Abukur, ya karanta bukatar samar da gundumar, yayin da mamba mai wakiltar Karamar Hukumar Mai’adua, Hon. Mustapha Rabe Musa Maiadua, ya yiwa majalisar bayani kan mahimmancin kirkirar sabuwar gundumar.
Bayan tattaunawa, Majalisar gaba daya ta amince da kirkirar gundumar, kuma ta amince da ita daidai da dokar kananan hukumomin jihar Katsina.
A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa masarautar Daura ta nada wa dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf, sarautar Talban Daura.
Babban mai ba Shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da labarin nadin da aka yiwa Yusuf a yau Talata, 20 ga watan Yuli a wani wallafa da yayi a shafinsa na Facebook.
Ya wallafa hoton shi, Yusuf, da Musa Daura, wanda ke dauke da taken:
"Tare da Yusuf Buhari, mai suna Talban Daura da Musa Daura, Dan Madamin Daura."
Asali: Legit.ng