An nada wa dan Shugaba Buhari, Yusuf, sarautar Talban Daura

An nada wa dan Shugaba Buhari, Yusuf, sarautar Talban Daura

  • Yayin da Musulmai ke bikin babban Sallah na wannan shekarar, an bai wa Yusuf Buhari sarautar gargajiya 'Talban Daura'
  • An hango dan shugaban na Najeriya sanye da kayan sarauta yayin da yake daukar hoto tare da Musa Daura da Garba Shehu
  • Idan abubuwa suka tafi kamar yadda aka tsara, ba da dadewa ba Yusuf zai auri 'yar sarkin Bichi a Kano, Zarah

Masarautar Daura ta nada wa dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf, sarautar Talban Daura.

Babban mai ba Shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da labarin nadin da aka yiwa Yusuf a yau Talata, 20 ga watan Yuli a wani wallafa da yayi a shafinsa na Facebook.

KU KARANTA KUMA: Eid-el-Kabir: Bidiyo ya nuna Buhari yana tafiya zuwa filin Idi a Daura yayin daama'a ke taya shi murna

Ya wallafa hoton shi, Yusuf, da Musa Daura, wanda ke dauke da taken:

Kara karanta wannan

Eid-el-Kabir: Bidiyo ya nuna Buhari yana tafiya zuwa filin Idi a Daura yayin daama'a ke taya shi murna

"Tare da Yusuf Buhari, mai suna Talban Daura da Musa Daura, Dan Madamin Daura."

An nada masa sarautar ne tare da Musa Daura, wanda yanzu shine Dan Madamin Daura.

An tattaro cewa sarautar Talban Daura babban matsayi ne a masarautar Daura ta jihar Katsina.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a watan Agustan da ya gabata, Sarkin Daura, Umar Farouq, ya bai wa Shugaban Guinea, Alpha Conde sarautar ta ‘Talban Daura’.

Farouq ya ce an bai wa Shugaba Conde sarautar ne saboda kaunar da yake nuna wa Buhari.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi

Da yake bayyana dalilin aikata abun da ya yi, Sarki Farouq ya ce, “Shugaba Conde ya bar dukkan jadawalin ayyukansa a kasarsa don bikin Idi-el-Kabir tare da takwaransa, Shugaba Buhari a Daura."

Buhari ya tura tawaga gidan Sarkin Bichi don sa ranar auren 'dansa Yusuf

Kara karanta wannan

Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari

A baya mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika tawagar wakilansa domin ganawa da iyalan Sarkin Bichi kan sa ranar daurin auren 'dansa, Yusuf Buhari, da Zahra Bayero.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa wannan tawagar da Buhari ya tura ta hada da gwamnoni, Ministoci, da Dirakta Janar da hukumar DSS, Yusuf Bichi.

An tattaro cewa tuni wasu sun dira jihar Kano da kayayyakin sa rana irinsu goro, da sauransu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel