Auren Yusuf Buhari: An kaddamar kwamitin mutane sama da 100 don kula da daurin aure

Auren Yusuf Buhari: An kaddamar kwamitin mutane sama da 100 don kula da daurin aure

  • Rahoto ya shaida cewa, an nada kwamitin mutane sama da 100 domin daurin auren dan shugaba Buhari
  • Sarkin Bichi, mahaifin diyar da Yusuf Buhari zai aura ne ya fitar da wata sanarwa dake tabbatar da haka
  • Hakazalika, za a yi nadin sarautar sarkin Bichi bayan daurin auren na Yusuf Buhari da Zahra Ado-Bayero

Jihar Kano - An kammala shirye-shiryen daura auren Yusuf, dan shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), tare da diyar Sarkin Bichi, Gimbiya Zahra Ado-Bayero, a ranar 20 ga watan Agusta, Reuben Abati ya ruwaito.

Mai magana da yawun masarautar Bichi, Lurwanu Malikawa, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado-Bayero, ya kaddamar da wani kwamiti na mutum 145 don saukaka bikin auren ba tare da matsala ba.

Sanarwar ta yi nuni da cewa Hakimin Bagwai, Nura Ahmad (Madakin Bichi) ne zai jagoranci kwamitin, tare da Abba Waziri (Falakin Bichi), a matsayin sakatare.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Auren Yusuf Buhari: An kaddamar kwamitin mutane sama da 100 don kula da daurin aure
Masarautar Bichi | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Yayin da yake kaddamar da kwamitin, sarkin, wanda Madakin Bichi ya wakilta, ya umarci mambobinta da su yi amfani da kwarewar da suka samu don tabbatar da nasarar bikin auren.

Ranar da za a daura da kuma ranar nadin sarauta

A cewar sanarwar, kwamitin zai kuma shirya nadin sarauta na Sarkin Bichi, gami da gabatar da sandar sarauta da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje zai yi masa.

Har ila yau, sanarwar ta nuna cewa za a gudanar da bikin auren a ranar 20 ga watan Agusta kuma an shirya yin nadin ne a ranar 21 ga watan Agusta a fadar Sarkin Bichi.

An ruwaito cewa Yusuf ya hadu da Zahra ne a kasar Ingila, inda suka yi karatun digiri na farko, jaridar Punch ta ruwaito.

Zarah Ado Bayero: Abin da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano da Yusuf Buhari zai aura

A wani labarin, an fara shirye shiryen auren dan gidan Shugaban kasa Muhummadu Buhari, Yusuf Buhari gadan gadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gaisuwar Sallah: Wasu ‘Yan Majalisar Tarayya da Gwamnoni 11 sun ziyarci Garin Daura

Ranar Lahadi, wakilcin shugaban kasa suka ziyarci fadar Sarkin Kano inda aka tattauna batun auren.

Gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru, shine ya jagoranci tawagar shugaban kasa zuwa fadar shugaban kasa tare da wasu manyan kusoshin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel