'Yan sanda sun bankado yunkurin harin 'yan bindiga, sun ceci mutum 8 a Katsina

'Yan sanda sun bankado yunkurin harin 'yan bindiga, sun ceci mutum 8 a Katsina

  • Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina tace ta bankado harin da ‘yan bindiga suka kai karamar hukumar Batsari
  • Kakakin hukumar, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a a jihar Katsina
  • Ya kara da bayyana yadda DPO din Batsari ya aika ‘yan sanda suka bude wuta har suka ceto mutane 8

Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta bankado harin da ‘yan bindiga suka kai karamar hukumar Batsari dake jihar.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, Kakakin hukumar na jihar, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a.

KU KARANTA: FG bata mika bukatar dawo da Igboho Najeriya ba yayin da kotu a Kwatano ta tsare shi

'Yan sanda sun bankado yunkurin harin 'yan bindiga, sun ceci mutum 8 a Katsina
'Yan sanda sun bankado yunkurin harin 'yan bindiga, sun ceci mutum 8 a Katsina. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sa kai zasu jagoranci yaki da 'yan bindiga a Sokoto, Tambuwal

A cewarsa: “A ranar Juma’a, 23 ga watan Yulin 2021 da misalin karfe 2:30, ‘yan bindiga suka rufe hanyar Jibia zuwa Batsari daidai kauyen Kabobi dake karamar hukumar Batsari da baburansu dauke da bindigogi kirar AK 47.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai

“Yan bindigan sun kai farmaki sannan sun yi garkuwa da mazauna kauyen a baburansu inda suka tsere dasu cikin daji.

“Bayan jin labarin hakan, DPO din Batsari ya ja tawagar yaransa masu inkiya da “Sharan Daji” suka bisu inda suka yi ta musayar wuta har suka samu nasarar ceto mutane 8.

“Cikin wadanda suka ceto daga hannun ‘yan ta’addan akwai tsoho mai shekaru 70, yarinya mai shekaru 13 da kuma yara 3 masu shekaru 12 duka ‘yan kauyen Inu dake karkashin karamar hukumar Batsari.

“Sannan sun ceci wata mata mai shekaru 20 da yaranta 2 mazauna Turaku Quaters a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina.”

Ya kara da bayyana yadda yanzu haka hukumar ta tura ‘yansanda suna cigaba da neman sauran mutane 3 da suke hannun ‘yan bindigan, Daily Trust ta wallafa.

A wani labari na daban, wata babban kotun tarayya dake zama a Abuja a ranar Juma'a ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kawo hadiman Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho su 12 kafin ranar 29 ga watan Yulin 2021.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

Mai shari'a Obiora Egwuatu ya bada umarnin bayan lauya Pelumi Olajengbesi ya shigar da kara mai lambar rijista FHC/ABJ/CS/647/2021 mai kwanan wata 7 ga watan Yuli kuma aka mikata a ranar 8 ga watan Yuli.

Egwuatu ya kara da baiwa 'yan sandan sirrin umarnin zuwa gaban kotun tare da sanar da dalilin hana belin wadanda aka adana, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel