Yan Bindiga Sun Saku Wasu Daga Cikin Daliban Sakandiren Bethel Baptist da Duka Sace a Kaduna
- Yan bindiga sun sako ɗalibai 28 daga cikin waɗanda suka sace a makarantar sakandiren Bethen Baptist Kaduna
- Shugaban ƙungiyar kiristoci reshen jihar Kaduna, Joseph Hayap, shine ya tabbatar da haka ranar Lahadi
- A baya dai wasu ɗaliban makarantar sun gudo daga hannun yan bindigan da suka sace su
Yan bindiga sun sako ɗalibai 28 daga cikin waɗanda suke sace a makarantar sakandiren Bethel Baptist Damishi, Jihar Kaduna, bayan shafe kwanaki 20, kamar yadda punch ta ruwaito.
Shugaban ƙungiyar kiristoci CAN reshen Kaduna, Joseph Hayab, shine ya tabbatar da sako ɗalibai yau Lahadi.
Adadin ɗalibai 121 ne yan bindiga suka yi awon gaba da su a ɗakin kwanansu ranar biyar ga watan Yuli.
Yan sanda sun kuɓutar da ɗalibai uku
The cable ta ruwaito cewa a ranar 12 ga watan Yuli jami'an yan sanda suka kuɓutar da ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna, Abraham Aniya tare da wasu ɗalibai biyu da yan bindiga suka sace a kan hanyar Kaduna-Kachia.
Kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya bayyana cewa:
"A ranar 12 ga watan Yuli da karfe 3:40 na yamma jami'an yan sanda tare da yan sa kai na JTF suka fita sintiri a dajin ƙauyen Tsohon Gaya, Chikun LGA, jihar Kaduna."
"A wannan fitar ne jami'an suka gano wasu ɗalibai uku da aka sace a dajin, sun yi.matukar gajiya kuma jikinsu ba karfi."
Dalibai biyu sun gudo
Hakazalika, a ranar 20 ga watan Yuli wasu ɗalibai biyu suka samu nasarar tserowa daga inda barayin ke tsare da su yayin da suka umarce su da su samo musu icce a cikin dajin.
Da yake tabbatar da lamarin ASP Jalige, yace jami'ai sun ga ɗaliban biyu a yankin Rijanna dake kan hanyar Kaduna-Abuja.
"Eh, mun samu nasarar kuɓutar da ɗalibai biyu da yammacin nan a kan hanyar Kadun-Abuja, kuma a halin yanzun an kai su asibiti domin duba lafiyarsu." inji shi.
Shugaban mabiya ɗarikar Baptist (NBC), Israel Akanji, ya tabbatar da cewa ba za'a biya kuɗin fansa ba domin sako ɗaliban.
Asali: Legit.ng