'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari
- Yan bindiga sun sace mata 13 a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna
- Matan suna cikin motocci uku ne suna hanyarsu ta zuwa bikin aure a Birnin Gwari
- Wani jagora a unguwa, Mohammed Umar, ya tabbatar da afkuwar lamarin
Yan bindiga sun sace mata 13 a tsakanin garuruwan Manini da Udawa da ke kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, a hanyarsu ta zuwa bikin daurin aure, Daily Trust ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis misalin karfe 12 na rana a lokacin da yan bindigan suka tare motocci uku da ke dauke da matan a hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.
DUBA WANNAN: 'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023
An gano cewa cikin wadanda aka sace din akwai mata masu shayarwa da wata mata da yayanta mata biyar.
An kuma ruwaito cewa akwai wani yaro dan makaranta mai shekaru bakwai a cikinsu.
Wani jagoran mutane a unguwa ya tabbatar da sace matan
Wani shugaba a unguwarsu, Mohammed Umar, ya shaidawa Daily Trust cewa dukkan matan yan asalin garin Udawa ne a karamar hukumar Chikun.
Ya ce:
"Dukkan matan 13, mafi yawancinsu matan aure, sun fito ne daga Udawa suna hanyarsu na zuwa Birnin Gwari domin hallartar bikin aure.
"Wasu daga cikinsu yan gida daya ne kamar Zainab Abu Jibril, uwargidan Malam Jibril Ibrahim da yaranta mata biyar dukkansu an sace su tare da wasu da ga wasu gidajen da yaransu kanana."
A cewarsa, idan ba domin sojoji sun kawo dauki cikin gaggawa ba da masu garkuwar sun sake sace wasu mutanen domin sun tare hanya ne suna kwasan wadanda suke so.
An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed amma bai amsa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.
Sojoji sun kama ɗan aiken ISWAP da aka tura Legas ya siyo wa 'yan ta'adda kaya
Hedkwatar tsaro ta sojojin Nigeria ta ce dakarun Operation AWATSE sun kama wani Ibrahim Musa da ake zargin dan kungiyar ta'addanci na ISWAP ne a yankin Sango Otta a jihar Ogun, The Cable ta ruwaito.
A yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi kan ayyukan rundunar daga ranar 18 zuwa 30 ga watan Yuni, Bernard Onyeuko, mukadashin direktan watsa labarai na sojoji ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin sintiri a unguwa Majidun a jihar inda aka kama Musa.
A cewarsa, bayannan sirri ya nuna cewa an tura Musa zuwa Legas ne domin ya siyo wa kungiyar ta ISWAP wasu kayayyaki da suke amfani da su a Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng