‘Yan fashi sun afkawa makaranta a Kaduna, sun sace takardun jarrabawar NECO suna tunanin kudi ne
- ‘Yan fashi da makami sun yi awon gaba takardun tambayoyin jarrabawar NECO bisa zaton kunshin kudade ne a Jihar Kaduna
- Bayanai sun ce tun daga banki ‘yan fashin suke bibiyar jami’ar hukumar NECO kan tunanin kudade ne ta karbo
- Iyayen daliban makarantar sun ce da farko an fada musu cewa maharan sun shiga makarantar da zimmar sace daliban
Jaridar Tribune ta rahoto wadansu ‘yan fashi da makami a safiyar ranar Juma’a sun kai hari kan makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Unguwar Sarki, a cikin garin Kaduna inda suka tafi da takardun jarrabawa da aka shirya wa daliban aji shida wadanda za su rubuta jarrabawar karshe ta NECO bisa tsammanin cewa kudade ne.
‘Yan bindigar da suka kutsa kai cikin makarantar sun nemi jami’ar da ke mai kula da NECOn da ta mika musu takardun jarrabawar duk da cewa ta yi kokarin bayyana musu takardun jarrabawar ne ba kudade ba.
An gano cewa sun kwace takardun jarrabawar da ke nannade a cikin kunshi tare da takardun amsa jarrabawar inda suka tafi da su.
Shugabar makarantar, Hajiya Bilkisu Aliyu, ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da manema labarai inda ta ce ‘yan bindigar sun bi diddigin Jami’an NECOn ne daga wani bankin da ke kan titin Alkali Road inda ta je karbar takardar jarrabawar da kuma takardun rubuta amsa.
Tace:
“Da yake sun yi tunanin cewa kudade ne, sai suka bukaci ta mika musu kunshin takardun da aka nade inda suka yi barazanar harbin ta.
“An gaya masu cewa ba kudi ba ne amma ba su saurara ba. Sun fizge takardun sannan suka bace bat,”.
Iyaye sun yi tunanin an zo garkuwa da yaransu ne
A halin yanzu, wani mahaifi, Sanusi Umar wanda dansa na daga cikin wadanda ke rubuta jarrabawar ya ce,
“Abin da muka ji da farko ‘yan fashi sun zo sace dalibanmu. Don haka daruruwan iyaye suka mamaye makarantar.
“Amma da zuwa makarantar, sai aka ce mana ‘yan fashi da makami ne suka zo suka tafi da takardun tambayoyin jarrabawar da aka nade a zaton su kunshin kudade ne.
"Ina son kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su karfafa tsaro a makarantu tunda wadannan masu aikata laifuffuka a yanzu suna kai wa makarantunmu hari."
Haka nan, an jiyo cewa makarantar da ma'aikatan NECO dole ne su tattara takardun jarrabawar daga wasu cibiyoyin domin bai wa wadannan daliban damar rubuta jarrabawar karkashin tsauraran matakan tsaro.
Asali: Legit.ng