Hoton Matar Da Ta Haɗa Baki Da Mijinta Don Ƙaryar Garkuwa Da Ita a Jihar Niger

Hoton Matar Da Ta Haɗa Baki Da Mijinta Don Ƙaryar Garkuwa Da Ita a Jihar Niger

  • Jami'an yan sanda sun kama mata da mijinta a jihar Niger bisa laifin hadin baki da garkuwa
  • Matar ta amsa cewa ta hada baki da mijinta don yin garkuwar karya inda mahaifinta ya biya N1m kudin fansa
  • Shima mijin matar ya amsa cewa sun hada baki ne suka yi garkuwar da taimakon wani abokinsa mai suna Abdullahi

Yan sandan jihar Niger sun kama wani Mohammed Mohammed mai shekaru 39 da matarsa Sadiya Ibrahim Umar mai shekaru 31 bisa laifin hadin baki da garkuwa, rahoton Daily Trust.

Idan za a iya tunawa, a ranar 15 ga watan Yulin 2021, an samu rahoton cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun sace Sadiya a Challenge Junction, Maitumbi zuwa hanyar tsohon filin tashin jirage bayan ta taso daga aiki a makarantar Umar Bn khattab International School, Maitumbi.

An Kama Mata Da Ta Haɗa Baki Da Mijinta Don Ƙaryar Garkuwa Da Ita a Jihar Niger
Mohammed Mohammed da matarsa Sadiya da suka shirya garkuwar karya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Bayan kwana daya da sace ta, wani ya kira mahaifinta a wayar tarho ya nemi a biya Naira miliyan 5 don fansarta daga baya aka rage kudin zuwa Naira miliyan 1 sannan aka ajiye a wani wuri a Rafin Yashi a Minna don mai garkuwar ya dauka.

Kara karanta wannan

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

Sadiya ta dawo gida a ranar 21 ga watan Yuli sannan rundunar yan sanda suka gayyace ta domin amsa tambayoyi.

Yadda yan sanda suka gano karyar ma'auratan

Kakakin yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce Sadiya ta amsa cewa ta hada baki da mijinta Mohammed don yin garkuwar karya da ita aka kaita kauyen Nugupi wurin abokin mijinta.

Kakakin yan sandan ya ce mijin ya amsa cewa ya karbi wayan matarsa ya mika wa wani abokinsa Abdullahi, wanda shine ya yi cinikin kudin fansar a madadinsa.

Ya ce ana cigaba da bincike kan lamarin sannan ana neman Abdullahi don kama shi, su kuma wadanda ke hannu za a gurfanar da su gaban kotu daba bisani.

Kakakin yan sandan ya ce:

"Wannan shine karo na uku da ake yin irin wannan garkuwar karyar a baya-bayan nan."

'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari

Kara karanta wannan

Hayaƙin Janareto Ya Kashe Mutum Huɗu Ciki Har Mata Da Mijinta Yayin Bikin Sallah a Kwara

A wani labarin, yan bindiga sun sace mata 13 a tsakanin garuruwan Manini da Udawa da ke kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, a hanyarsu ta zuwa bikin daurin aure, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis misalin karfe 12 na rana a lokacin da yan bindigan suka tare motocci uku da ke dauke da matan a hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

An gano cewa cikin wadanda aka sace din akwai mata masu shayarwa da wata mata da yayanta mata biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel