Da duminsa: Kotu a Kano ta haramtawa majalisar jiha binciken Rimingado

Da duminsa: Kotu a Kano ta haramtawa majalisar jiha binciken Rimingado

  • Wata babbar kotun jihar Kano ta tsawatarwa majalisar jihar Kano kan bincikar Rimingado
  • Kotun karkashin jagorancin Mai shari'a Sanusi Ma'aji ta ce sai ta kammala shari'ar kafin a cigaba
  • Idan mun tuna, Muhuyi Magaji ya samu gayyata daga majalisar jihar kan wani koke da aka mika a kansa

Wata babbar kotu a jihar Kano wacce ta samu shugabancin Mai Shari'a Sanusi Ma'aji, ta hana majalisar jihar Kano bincikar tsohon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa, PCACC, Muhuyi Magaji, har sai an kammala shari'a.

Majalisar jihar Kano ta gayyaci Rimingado da ya bayyana gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar domin bincikar korafin da aka kai na ranar Laraba, 14 ga watan Yulin 2021, Solacebase ta wallafa.

KU KARANTA: An kaiwa shugaban kasan rikon kwaryan Mali farmaki a filin Idi

Da duminsa: Kotu a Kano ta haramtawa majalisar jiha binciken Rimingado
Da duminsa: Kotu a Kano ta haramtawa majalisar jiha binciken Rimingado. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Amma Rimingado yayin dogaro da rashin lafiyar da yake fama da ita kuma ya bayyana bayanin likita a rubuce, ya bukaci asalin kwafin korafin da majalisar ta samu a kansa wanda hakan yasa ta bukaci ya bayyana a gabanta.

Kara karanta wannan

An kaiwa shugaban kasan rikon kwaryan Mali farmaki a filin Idi

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, kotun a ranar Juma'a, ta yanke wadannan hukuncin:

"Umarnin dakatar da bincike na wucingadi ya karbu inda aka bukaci kada a sake bincikar mai karar kan lamari mai alaka da hakan har sai kotu ta kammala shari'ar.

"Kotu ta bada umarnin a gaggauta jin shari'ar cikin lokaci."

Alkalin ya dage sauraron karad zuwa ranar 6 ga watan Augustan 2021.

KU KARANTA: Zamfara: Yari ya caccaki Buni, yace bai aminta da kwamitin rikon kwaryan APC ba

A wani labari na daban, mai rajin kafa kasar Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya gurfana a gaban wata kotun daukaka kara ta Kwatano saboda matsalar da ta hada da hukumar shige da ficen kasar.

Kotun ta bukaci a cigaba da tsare mata Igboho a yayin da za ta cigaba da sauraron karar a ranar Juma'a, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ndume na rokon kotu da ta tsame shi daga shari'ar Maina, ta bashi kadarorinsa

Amma kuma, matarsa, Ropo, wacce 'yar asalin kasar Jamus ce an saketa domin kotun tace bata kama ta da wani laifi ba.

Igboho da matarsa sun shiga hannun hukuma ne yayin da suka dira filin sauka da tashin jiragen sama a Cardinal Bernardin dake Kwatano a ranar Litinin yayin da suke hanyarsu ta zuwa Jamus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel