Da duminsa: Kotu ta umarci DSS da su gabatar da mukarraban Igboho 12 da suka tsare
- Babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta bukaci jami'an DSS da su gabatar da hadiman Igboho 12 dake hannunsu
- Kamar yadda mai shari'a Obiora Egwuatu ya bayyana a kotun a ranar Juma'a, yace yana son ganinsu nan da 7 ga watan Yuli
- Idan zamu tuna, an yi musayar ruwan wuta tsakanin jami'an DSS da hadiman Igboho a yankin Soka dake Ibadan
Wata babban kotun tarayya dake zama a Abuja a ranar Juma'a ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kawo hadiman Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho su 12 kafin ranar 29 ga watan Yulin 2021.
Mai shari'a Obiora Egwuatu ya bada umarnin bayan lauya Pelumi Olajengbesi ya shigar da kara mai lambar rijista FHC/ABJ/CS/647/2021 mai kwanan wata 7 ga watan Yuli kuma aka mikata a ranar 8 ga watan Yuli.
KU KARANTA: Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno
Egwuatu ya kara da baiwa 'yan sandan sirrin umarnin zuwa gaban kotun tare da sanar da dalilin hana belin wadanda aka adana, Daily Nigerian ta ruwaito.
Idan zamu tuna, a kalla an damke mutum 12 daga cikin mukarraban Igboho kuma DSS ta adana su a samamen da suka kai ranar 1 ga watan Yuli a yankin Soka na Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Jami'an tsaron farin kaya sun ce sun harbe mutum biyu daga cikin mukarraban Igboho bayan musayar wutar da suka yi wanda har ya kai ga Igboho ya tsere, jaridar punch ta ruwaito.
Daga bisani an bayyana ana nemansa ido ruwa jallo kan zarginsa da tara miyagun makamai a gidansa, lamarin da ya musanta.
KU KARANTA: Boko Haram: An baiwa dakarun sojin Najeriya sabon umarni kan yakar ta'addanci
A wani labari na daban, an kaiwa Shugaban kasan rikon kwarya na kasar Mali, Assimi Goita, farmaki yayin sallar dinin babbar sallah, kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito.
Ta samu labarin ne daga ofishin shugaban kasa, inda tace harin ya faru ne a babban masallacin kasar dake Bamako.
"Tuni jami'an tsaro suka fi karfin mai kai farmaki kuma an fara biincikar lamarin," fadar shugaban kasan ta wallafa a shafinta na Twitter.
Asali: Legit.ng