‘Yan bindiga sun kashe mutum 18 a wasu jihohin arewa biyu

‘Yan bindiga sun kashe mutum 18 a wasu jihohin arewa biyu

  • Wasu 'yan bindiga suka kai farmaki wasu garuruwan Benuwai da Nasarawa inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 da asarar dukiyoyi
  • A jihar Benuwe, maharan sun far ma al'umma a wasu garuruwa da ke yankin Guma inda suka halaka mutane 13
  • Sannan a jihar Nasarawa mutane biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon harin

Hare-hare da dama da ‘yan bindiga suka kai a kan al’ummomin Benuwai da Nasarawa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 da asarar dukiyoyi.

A ranar Talata, an tattaro cewa kimanin mutane 13 aka kashe lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wasu garuruwa a yankin Guma da ke Benue.

An kuma rahoto cewa maharan sun kuma auka wa garin na Torkula.

‘Yan bindiga sun kashe mutum 18 a wasu jihohin arewa biyu
‘Yan bindiga sun kashe mutum 18 a Benuwe da Nasarawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Caleb Abs, shugaban karamar hukumar Guma ya ce kimanin mutane 13 aka kashe a duka hare-haren biyu, jaridar The Nation ta ruwaito.

“Gaskiya ne cewa an kai hari a jiya. Anyi jana’iza a garin Torkula kuma mutane da suka dawo daga binne mamatan sun fuskanci hari kuma kimanin mutane biyar aka kashe,” inji shi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda Huɗu a Enugu

“Misalin karfe 10 na daren jiya, an sake kai wani hari a Branch Ude inda aka kashe kimanin mutane takwas.
"Mutane biyu sun ji rauni bisa ga bayanin da na samu, kuma yanzu haka suna karbar magani a asibiti."

Jaridar ta kuma ruwaito cewa a Nasarawa, ‘yan sanda sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe manoma yan kabilar Tiv biyar.

Harin ya afku ne a kauyen Gidan Sule da ke Karamar Hukumar Keana na jihar da sanyin safiyar jiya.

An tabbatar da kisan ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Lafia ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa (PPRO), ASP Ramhan Nansel.

A cewar kakakin rundunar na jihar Nasarawa:

“A ranar 21/7/2021 da misalin karfe 2300hrs, an samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, yayin da suke harbi ba kakkautawa, sun kai hari kan wani Ofishin da ke kauyen Gidan Sule a kan hanyar Lafia-Makurdi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

“Bayan samun wannan bayanin, an tura jami’an tsaro da suka kunshi rundunar ‘yan sanda ta tafi da gidanka, masu yaki da ta’addanci, yan banga da maharba, tare da tallafi daga Sojoji inda suka fatattaki maharan."

Ya ci gaba da cewa an gano gawarwaki hudu a wurin, yayin da uku daga cikin wadanda suka jikkata aka tsamo su kuma aka garzaya da su asibitin Odumu don kula da lafiyarsu; mutum daya daga baya ya mutu yayin karbar magani a asibiti.

A wani labarin, rundunar yan sandan jihar Zamfara ta ce ta kashe wani hatsabibin dan bindiga a jihar sannan ta ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kakakin yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai ranar Alhamis a Gusau.

Ya bayyana cewa yayin artabun an kashe dan bindiga daya kuma nan take aka ceto mutum 11 cikin wadanda yan bindiga suka sace.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace wasu mata da shanu masu yawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel