Tashin Hankali Yayin da Wasu Yan Bindiga Suka Hallaka Manoma 5 a Jihar Nasarawa

Tashin Hankali Yayin da Wasu Yan Bindiga Suka Hallaka Manoma 5 a Jihar Nasarawa

  • Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kashe manoma yan kabilar Tiv guda 5 a ƙauyen Gidan Sule, jihar Nasarawa
  • Lamarin ya faru ne da daren ranar Laraba, inda maharan suka mamayi mutanen ƙauyen lokacin da suka kwanta bacci
  • A halin yanzun an jibge jami'an yan sanda, bijilanti, mafarauta da kuma dakarun sojin ƙasa domin tabbatar da komai ya dai-daita

Aƙalla manoman kabilar Tiv guda biyar ne wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne suka kashe a ƙauyen Gidan Sule, karamar hukumar Keana, jihar Nasarawa.

KARANTA ANAN: Zan Jingine Siyasa a 2023 Domin In Koma Aikin Tallafawa Mutane, Gwamnan Arewa

Shugaban ƙungiyar cigaban Tiv a jihar, Kwamared Peter Ahemba, shine ya bayyana haka a wata fira da dailytrust a Lafiya, babban birnin Nasarawa.

Ahemba yace maharan sun mamaye ƙauyen, inda suka kai hari kan mutanen da daddaren ranar Laraba yayin da mutane ke bacci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai

Yan bindigan sun hallaka mutum huɗu nan take yayin da ragowar ɗayan ya karisa bayan an kai shi asibiti.

Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Nasarawa
Tashin Hankali: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma 5 a Jihar Nasarawa Hoto: 24ureports.com
Asali: UGC

Yace: "Mutum 5 muka rasa a wani harin yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne a ƙauyen Gidan Sule ranar Laraba da daddare."

"Huɗu daga ciki sun mutu nan take yayin da ɗayan akai tsammanin zai tashi, amma daga baya ya karisa a asibiti."

"Mutanen Nasarawa masu son zaman lafiya ne. Babu wani rashin jituwa tsakanin yan kabilarmu da waɗanda ake zargin fulani makiyaya ne a yankin, shiyasa nake mamakin meye dalilin kawo mana hari."

Ya kuma yi kira yan kabilarsa ta TIV da su kwantar da hankalinsu yayin da jami'an tsaro suke kokarin dawo da zaman lafiya a yankin.

Kungiyar fulani zata gudanar da bincike

Da aka tuntuɓe shi ta waya, shugaban ƙungiyar fulani Miyetti Allah reshen jihar Nasarawa, Bala Dabo, yace sam ba shi da labarin an kai hari a ƙauyen.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Amma yayi alƙawarin cewa zai gudanar da bincike kan lamarin domin tabbatar da waɗanda ke da hannu a kai harin.

"Ba'a sanar dani komai game da harin ba, saboda haka ba zan iya tabbatar da mutanen mu ne suka kai harin ba. Amma ina tabbatar muku da cewa zamu bincika don tabbatar da ainihin abinda ya faru ranar Laraba da daddare," inji shi.

KARANTA ANAN: Maganar da Sarkin Muri Ya Yi Ranar Sallah Kan Fulani Makiyaya Ta Bar Baya da Kura

Yan sanda sun fara ɗaukar mataki

Da yake tabbatar da lamarin a Lafiya, Kakakin yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, yace daga sanda hukumar ta samu rahoton harin aka ɗauki matakin tura yan sanda, jami'an tsaron bijilanyi, mafarauta tare da haɗin guiwar dakarun soji zuwa yankin.

Ya yi alƙawarin cewa za'a kamo yan bindigan dake da hannu a harin kuma a gurfanar da su domin hakan ya zama izina ga sauran mutane.

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga da Dama Yayin Wani Artabu a Neja

A wani labarin kuma Ba da Jimawa Ba Wasu Jiga-Jigan Gurbatattun Yan Siyasa Zasu Sauya Sheka Zuwa APC, Shugaban ADC

Shugaban ADC ta kasa, Mr. Nwosu, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan wasu gurbatattun yan siyasa zasu koma APC.

Jam'iyyar ADC ita ce wadda ta zo na uku a zaɓen 2019 da ya gabata a yawan kuri'u.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262