Talakawa na son Buhari: Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta cire rai a zaben 2023

Talakawa na son Buhari: Fadar shugaban kasa ta ce PDP ta cire rai a zaben 2023

  • Fadar shugaban kasa ta yi wajabi kan halin da zaben 2023 zai dauka, kasancewar talakawa na kaunar Buhari
  • Fadar ta caccaki PDP bisa yi wa 'yan Najeriya fatan karya kan mulkin APC musamman ta shugaba Buhari
  • A ci gaba da shirin babban zaben 2023, 'yan siyasa na ci gaba da jefo zantuka kan yadda za ta kaya

Fadar Shugaban kasa a ranar Talata ta fada wa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, da ta daina sa ran lashe babban zaben na 2023, saboda har yanzu talakawa za su yi wa Shugaba Muhammadu Buhari mubaya'a kuma ba za su taba yin watsi da shi ba.

An zargi PDP da ba ‘yan Najeriya fatan karya cewa saboda rashin tabuka abin a zo a gani a jam’iyyar APC, a matakin kasa, cewa (PDP) za ta karbi mulkin da ta rasa a hannun APC a shekarar 2023, Daily Nigerian.

Amma Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, wanda ya yi magana jim kadan bayan Sallar Idi a Daura ta Katsina, ya ce ’yan Najeriya sun sani daram kuma ba za su yarda wani bangare ya karbi mulki a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Talakawa na son Buhari: Fadar shugaban kasa ta fada wa PDP gaskiya kan zaben 2023
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

A cewarsa:

"Shugaban yana da goyon baya mara girgiza ba kawai a mahaifarsa ba har ma a duk fadin kasar kuma ya isa ga ‘yan adawa su yarda cewa Shugaban kasar yana da matukar muhimmanci ga jam’iyya mai mulki da 'yan Najeriya baki daya.
“Har ilayau, ya zama musu cikas ga siyasa da ba za su iya wargazawa a zaben 2023 ba.
"Mun yi imanin cewa PDP da sauran jam’iyyun adawa suna bakin ciki da fatan karya kan mulki a zaben 2023.
“Talakawa ba za su taba yin watsi da shugabancin Shugaba Buhari da APC ba. Ina tabbatar muku da cewa a 2023, talakawa za su jira Shugaban kasa ya nuna hanya cikin ladabi da abi da ya gina wa kasa ta fuskar samar da ababen more rayuwa da kuma jin dadin matasa a kasar.
"Babu wanda zai dauki kasada ta hanyar gayyatar wani bangare ya zo ya karbi mulki a 2023."

Kara karanta wannan

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana manya kan batun

Wani matashi dan shekaru 35 da ke neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar Kano, Malam Aminu Sa’idu, a jiya ya gana da mataimaka na musamman (SAs) ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje don sanar da su burinsa.

Da yake magana da Daily Trust bayan ganawar, matashin ya ce yana daga cikin shawarwarin da yake bi gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Ya kuma ce ganawar ta yi daidai da kudirin dake rajin ba matasa damar a dama dasu a mulki na"Not Too Young to Run", da kuma dabarun fadada aniyarsa zuwa dukkan sassan kasar.

Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

A wani labarin, Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa sojojin da suka ji rauni da ke yaki a yankin tallafin naira miliyan 10 a jiya Talata.

Kara karanta wannan

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne a yayin liyafar cin abincin rana da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya shirya a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.

Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun kan jajircewarsu da kuma jaddada alkawarin gwamnatinsa na ci gaba da ba su goyon baya har a cimma nasara a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.