Jigon PDP ya ambaci sunayen jiga-jigan ‘Yan siyasa 2 da yake tsoro daga APC a zaben 2023

Jigon PDP ya ambaci sunayen jiga-jigan ‘Yan siyasa 2 da yake tsoro daga APC a zaben 2023

Segun Sowunmi ya fadi wadanda za su iya kawo wa PDP matsala a zaben 2023

‘Dan adawar ya ce Bola Tinubu da Yahaya Bello ne yake tsoro a Jam’iyyar APC

Sowunmi ya bayyana cewa Bola Tinubu ya taimakawa Buhari ya hau kan mulki

Daya daga cikin manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya zauna da Channels TV, aka yi hira da shi game da Muhammadu Buhari da siyasar Najeriya.

Mista Segun Sowunmi ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba wani barazana ba ne ga jam’iyyar hamayya ta PDP a zabe mai zuwa na 2023.

“Buhari ba matsala ba ne, wannan karamin alhaki ne."

KU KARANTA: Matashi ya na sha'awar yin takarar Shugaban kasa a 2023

Bola Tinubu da Yahaya Bello su ne abin tsoro

Da aka yi hira da ‘dan siyasar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli, 2021, ya bayyana wasu daga cikin ‘ya 'yan APC da za su iya kawo wa PDP matsala a zabe na gaba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya hana Fasto Bakare zama Mataimakin Buhari a zaben 2015, ya kakabo Osinbajo

“Akwai mutane biyu a jam’iyyar APC da su ke ba ni ciwon kai.”
“Na damu da gwamna Yahaya Bello domin ina duba sawunsa, matashi ne, kuma ya san wadanda zai tuntuba, su saurare shi.”
“Sannan kuma hankali na ya tashi da Bola Ahmed Tinubu, saboda na san irin mutanen da ya kafa a siyasa.”

Buhari karamin alhaki ne - Sowunmi

Buhari ya yi takara sau uku ya sha kashi kafin 2015 da tazarcensa a 2019, Segun Sowunmi ya na ganin albarkacin Tinubu ne har Buhari ya zama shugaban kasa.

KU KARANTA: Boko Haram da ‘Yan bindiga sun kashe mutum 1, 030 a Jihohi 34

Bola Tinubu da Yahaya Bello
Bola Tinubu da Gwamnan Kogi, Bello
Asali: UGC

“Jam’iyyar APC ba ta doke PDP a 2015 saboda ta na APC ba, ta ci zabe ne a 2015 da 2019 saboda goyon bayan tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu.”

Sowunmi ya ce Buhari ya gaza cika alkawuran da ya dauka na inganta tsaro, habaka tattali da yaki da rashin gaskiya, don haka mutane ba za su yi APC a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Yari ya ce wasu 'Yan siyasan Arewa na kokarin hana shi zama Shugaban APC

“A lokacin da mu ke da matsaloli a kasa, ya yi wuri mu rika maganar zabe tun a yanzu.”

A makon nan ne aka samu rahoto cewa Gwamnan jihar Ribas, Mai girma Nyesom Wike ya ajiye adawarsa a gefe, ya yabi Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnatin tarayya ta amince da rokon Gwamna Wike na gina makarantar koyon aikin shari’a, kuma an karbi wannan bukata, har ta kai an fara ginin makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel