Ahmed Musa na shirin sanya hannu kan yarjejeniyar miliyoyin naira tare da kungiyar Turkiyya

Ahmed Musa na shirin sanya hannu kan yarjejeniyar miliyoyin naira tare da kungiyar Turkiyya

  • Ahmed Musa na iya gudanar da kasuwancinsa a kungiyar Fatih Karagumruk ta kasar Turkiyya idan rahotannin da ke yawo suka zama gaskiya
  • An tattaro cewa kyaftin din na Super Eagles ya amince da wasu yarjejeniya na kashin kansa don shiga kungiyar ta Istanbul
  • An yi ikirarin cewa tsohon dan wasan na Al-Nassr ta Saudiyya kuma tsohon dan wasan gaban na Leicester City zai isa Turkiyya a cikin kwanaki masu zuwa

Rahotanni sun kawo cewa kyaftin din Super Eagles na Najeriya Ahmed Musa ya amince da yarjejeniyar sirri kuma yana shirin komawa kungiyar Fatih Karagumruk ta Turkiyya.

Skorer ta jaridar The Nation ta ruwaito cewa tsohon dan wasan gaban na Leicester City da CSKA Moscow zai kammala shirin nasa a cikin kwanaki masu zuwa.

Ahmed Musa na shirin sanya hannu kan yarjejeniyar miliyoyin naira tare da kungiyar Turkiyya
Ahmed Musa na shirin komawa kungiyar Turkiyya Hoto: Catherine Ivill
Asali: Getty Images

Kungiyar Fatih Karagumruk na da zama ne a Istanbul babban birnin Turkiyya, amma har yanzu ba ta lashe wani babban kofi ba.

Kara karanta wannan

Bayan Kame Sunday Igboho, Yarbawa sun magantu kan ra'ayin ballewa daga Najeriya

Rahoton ya ci gaba da cewa Musa zai isa Turkiyya a cikin kwanaki masu zuwa don kammala shirinsa.

Zai sa hannu a matsayin wakili na kyauta bayan ya shafe tsawon watanni shida da suka gabata tare da kungiyar NPFL ta Kano Pillars, inda ya ba da taimako a wasanni tara. Ahmed Musa ya kasance yana da alaƙa da manyan kulob din Turkiyya kamar Galatasaray a baya.

Ya yanke shawarar komawa kungiyar kwallon kafa ta Pillars ne bayan ya kasa samun damar komawa kasar waje bayan ya bar kungiyar Al Nassr ta Saudi Arabia a bara.

Musa wanda ya nuna kishin kasa ya kuma bukaci fitattun taurarin kungiyar kwallon kafa na yanzu da na baya da su yi kokarin taka leda a kalla na kaka daya a Najeriya.

Musa ya bar kulob din Riyadh na Al –Nassr a 2020 tare da sauran shekaru biyu na kwangilan shekaru hudu da ya sanya wa hannu lokacin da ya koma cikinta daga Leicester City.

Kara karanta wannan

Duk da ba ayi wa Ibo adalci a Najeriya, ba za mu goyi bayan Biyafara ba – Dattijon Neja Delta

Ya fadawa ESPN cewa shawarar barin kungiyar gaba daya nasa ne amma bangarorin biyu sun sasanta tare da fahimtar juna.

Ahmed Musa ya auri dalleliyar sabuwar amarya

A gefe guda, a daren ranar Lahadi ne hotunan wata zukekiyar budurwa tare da fitaccen dan kwallon kafa Ahmed Musa suka bayyana a shafuka daban-daban na Instagram.

Kamar yadda shafin northern_hibiscus ya wallafa a daren Lahadin, shafin ya saka kyawawan hoton Ahmed Musa tare da wata doguwa farar budurwa mai kyau.

A wallafar ta ce: "Ga amaryar @ahmedmusa718. Kai, ina da abubuwa da yawa da nake son cewa, amma Ahmed Musa mutumina ne. Allah ya sanya alheri. Amarya kam sai da ka zaba ka dirje."

Asali: Legit.ng

Online view pixel