Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

  • Babban Bishop ya bayyana yadda ya gargadi 'yan Najeriya bisa zaben 2015 na shugaban kasa
  • Ya ce ya gargadi 'yan Najeriya kada su jefa kansu ga matsala ta hanyar zaben shugaba Buhari
  • Ya ce tuni ya hango dukkan matsalolin da kasar ke fuskanta saboda ubangijinsa ya nuna masa

Bishop David Oyedepo na cocin Living Faith, ya ce gabanin zaben 2015, ya gargadi ‘yan Najeriya game da zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC na wancan lokacin, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).

Malamin ya bayyana hakan ne yayin daya daga cikin hidimomin cocin a Canaanland dake Ota, jihar Ogun, a jiya Lahadi 18 ga watan Yuli

Ya ce ya yi daidai da ya yi gargadin kada Buhari ya hau mulki amma ‘yan Najeriya suka yi biris da gargadin “fuskantar matsala” na shugabancin Buhari

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

KARANTA WANNAN: Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015
Bishop David Oyedepo | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Oyedepo ya ce 'yan Najeriya da yawa sun yi fushi da shi a kan batun amma bayan shekaru shida na gwamnatin Buhari, wadanda suka soke shi sun ga 'bayyanar taurin kansu' wanda ya ce yana zura musu ido.

Legit.ng Hausa ta tattaro daga jaridar Sun, inda David Oyedepo ke cewa:

“Na sami dama na kasance cikin 'yan kadan da Allah ke nunawa abubuwa tun kafin su faru. Wasu mutane sun fusata dani lokacin da nake magana akan wannan muguwar gwamnatin.
"Na fada wa kasar nan, za ku jefa kanku ga matsala a shekarar 2015. Shin suna cikin matsala ne ko kuma cikin jin dadi a yanzu? Na ga an tilasta muguntar mugaye a cikin kasa.

Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

Wani dan rajin kare hakkin dan adam, Malcolm Emokiniovo Omirhobo, ya yi barazanar maka Shugaba Muhammadu Buhari a kotu game da bayar da lasisin mallakar bindiga kirar AK-47 don kare kai.

Omirhobo a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 8 ga Yulin 2021, ya bukaci shugaban da ya amince da mallakar bindigogi ga mutane don kare kansu, iyalai da dukiyoyinsu daga harin 'yan ta'adda masu rike da muggan makamai.

Da yake magana da Daily Trust, lauyan ya ce a shirye yake ya kalubalanci shugaban a kotu kan wannan batun a cikin kwanaki masu zuwa.

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

A wani labarin, Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma'aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na'ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar, sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel