Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari

Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya jadada cewa tsarinsa na tsamo yan Nigeria miliyan 100 daga talauci zai yiwu
  • Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a ranar Litinin yayin kaddamar da Gidan Gona na Zamani a jihar Katsina
  • Buhari ya ce babu dalilin da zai sa Nigeria ta dogara da man fetur a yayin da tana da yanayi mai kyau da kasar noma da al'umma masu yawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce har yanzu tsarinsa na fitar da yan Nigeria miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10 zai yiwu, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Lititin bayan kaddamar da Gonar Zamani a Suduje-Daura ta Hukumar Cigaban Kasar Noma ta Kasa, NALDA, a jihar Katsina.

Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah

The Cable ta ruwaito cewa Buhari yana kyautata zaton za a iya cimma wannan buri duba da yadda gwamnati da mutane ke hadin gwiwa wurin habbaka tattalin arziki ta hanyar amfani da noma.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa farashin kayan Masarufi yayi tashin gwauron zabi, Shugaba Buhari

Shugaba Buhari, cikin sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ya ce dogaro kan man fetur ya janyo koma bayan tattalin arziki tsawon shekaru saboda rashin tabbas na farashin man fetur da ke shafan kasafin kudi da aiwatar da shi.

Shugaban kasar ya ce abin da ya fi zama tabbas ga yan Nigeria shine noma, duba da Nigeria tana da yanayi mai kyau da kasar noma da kiwo tare da dimbin mutane da a shirye suke su koyi sabbin dabaru.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Takwas a Jirgin Ruwa

Ya ce:

"Ina son in jadada niyyata ta tsamo yan Nigeria miliyan 100 daga kangin talauci abu ne mai yiwuwa. Kasar mu na da yanayi mai kyau, kasan noma mai kyau da mutane da kayan aiki, tare da juriya da jajircewa irin ta matasa da ke son kawo sauyi a kasar.
"Za mu iya, kuma za mu yi. Babu wata hujja da za a iya bayarwa na cigaba da zama kasa da ke dogaro kan abu daya domin tafiyar da tattalin arzikinta duba da kallubalen sarrafa mai da hawa da saukan farashin mai a kasuwan duniya a yayin da muna da damar noma da kiwo."

Kara karanta wannan

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO Da Buhari ya naɗa

A wani labarin daban, kun ji Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarrabawar kasa ta NECO, Daily Trust ta ruwaito.

Mukadashin shugaba ne ya ke rike da hukumar tun bayan rasuwar tsohon shugabanta Farfesa Godswill Okeke.

Wata wasika mai kwana wata 16 ga wata Yulin 2021 dauke da lamba FME/PSE/NECO/1078/C.1/36 da sanya hannun ministan Ilimi, Adamu Adamu, ta ce an nada shi ne karo na farko na shekaru biyar daga ranar 12 ga watan Yulin 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel