'Yan Boko Haram da ISWAP 28 sun mika kansu ga rundunar sojin Najeriya

'Yan Boko Haram da ISWAP 28 sun mika kansu ga rundunar sojin Najeriya

  • Rundunar sojin Najeriya sun tabbatar da karbar mayakan Boko Haram da suka mika wuya
  • Rundunar ta bayyana cewa, mayakan sun gudu ne, amma daga baya suka dawo tare da iyalansu
  • Rundunar ta bayyana adadin 'yan Boko Haram da ISWAP din da suka mika wuya gareta

Rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram da na ISWAP 28 da iyalansu da suka tsere sun mika kansu ga dakarun rundunar bataliya ta 151 a jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, BBC ta ruwaito.

Sanarwar ta ce mayakan da suke tsere wa hare-haren sama da ake kai musu sun mika wuya ne ga dakarun bayan da aka fi karfinsu.

KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

'Yan Boko Haram da ISWAP 28 sun mika kansu ga rundunar sojin Najeriya
Taswirar jihar Borno | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Sanarwar ta kuma ce an kai mayakan da iyalansu wasu kauyukan wajen gari.

Kara karanta wannan

Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus

Sanarwar ta ce:

"Cikin su akwai maza 11 da mata biyar da ƴaƴansu 12. Sannan mun samu jigidar harsasai 27 da AK47 uku da sauran makamai."

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

Babban hafsan sojoji, Janar Faruk Yahaya, ya baiwa 'yan Najeriya tabbacin cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da mai da hankali wajen magance dumbin matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Yahaya ya bayar da tabbacin ne a sakonsa na fatan alheri ga hafsoshi, sojoji da danginsu kan bikin Babbar Sallah na 2021, ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, a Abuja.

Ya ce bikin na Babbar Sallah ya nuna kyawawan dabi'u na biyayya, mika kai da sadaukarwa wadanda su ne manyan kwarewa ta aikin sojoji, Punch ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

A wani labarin, A wani labarin, Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce harsasai da sauran karfin makamai su kadai ba za su iya dakatar da fashi da makami, bindiganci da sauran nau'ikan aikata laifuka a kasar ba.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno

Ya fadi haka ne a ranar Lahadi a Abuja yayin bikin cikar shekaru 50 na tsohon Corps Marshal na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Osita Chidoka.

A cewarsa, magance ta'addanci da aikata laifuka yana bukatar manyan shirye-shirye masu inganci na gwamnati, fasaha da sauran dabaru, Reuben Abati ya tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: