Gwamna Ya Caccaki Sanatocin APC, Ya Fadi Munafuncin da Suke Shiryawa a Zaben 2023

Gwamna Ya Caccaki Sanatocin APC, Ya Fadi Munafuncin da Suke Shiryawa a Zaben 2023

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya zargi sanatocin APC kan ƙin amincewa da tura sakamakon zaɓe ta Na'ura
  • Gwamnan ya gargaɗi duk wani wanda yake shirin maguɗin zaɓe a jihar Benuwai da ya zauna ya sake tunani
  • Ortom ya nuna rashin jin daɗinsa da dawo da kudirin samar da ruwa wanda shugaban ƙasa ya yi

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya zargi cewa mambobin jam'iyyar APC sun yi fatali da dokar tura sakamakon zaɓe ta na'ura ne saboda suna ƙulla-ƙullar maguɗin zaɓe a 2023, kamar yadda leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sako Sarki Mai Daraja Ta Daya da Suka Sace a Kogi

Gwamna Ortom, ya faɗi haka ne yayin wata fira da manema labarai, ya yi gargaɗin cewa jiharsa ta PDP ce, kuma duk wanda ke shirin maguɗin zaɓe a 2023 to ya sake tunani.

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom
Gwamna Ya Caccaki Sanatocin APC, Ya Fadi Munafuncin da Suke Shiryawa a Zaben 2023 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ortom, yace: "Na faɗa a baya zan sake nanatawa yanzun, jihar Benuwai ta PDP ce, kuma ba zamu bar kowaye yazo ya yi maguɗi a zaɓe a jihar mu ba."

Kara karanta wannan

Sanata Ahmad Lawan Ya Faɗi Dalilin da Yasa Sanatocin APC Suka Yi Fatali da Dokar Tura Sakamakon Zaɓe Ta Na'ura

"Saboda a jihar Benuwai, APC ba ta da goyon bayan jama'a, mutane PDP suke ƙauna, saboda haka duk wanda yayi ƙoƙarin canza sakamakon zaɓe mai zuwa za'a yi maganinsa."

A cewar gwamnan, masu zaɓe a jihar Benuwai suna da ilimi kuma sun san abinda suke yi, sannan a shirye suke a kowane lokaci su bada kariya ga ƙiri'unsu.

Kudiirin samar da albarkatun ruwa

Game da sabunta kudirin ruwa a majalisa, inda shugaban ƙasa ya buƙaci yan majalisun tarayya biyu su gaggauta amincewa da shi, Gwamna Ortom ya bayyana shirin da munafunci kuma ba zai taɓa karɓuwa ba.

KARANTA ANAN: Sanata Ahmad Lawan Ya Faɗi Dalilin da Yasa Sanatocin APC Suka Yi Fatali da Dokar Tura Sakamakon Zaɓe Ta Na'ura

"Yanzun kowa yana gani gwamnatin APC ba ta son alkairi ga yan Najeriya, kudirin da yan Najeriya sukanyi fatali da shi, har yan majalisun suka ƙi amincewa da shi, amma yanzun an ƙara dawo da shi, saboda me?" inji Ortom

Kara karanta wannan

Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Laƙume Rayukan Mutum 14 Tare da Jikkata Wasu a Osun

A cewar Gwamna Ortom, an dawo da ƙudurin ne domin ya maye gurbin samar da Rugar fulani makiyaya da kuma ƙara musu ƙarfin guiwa su cigaba da kiyon fili.

A wani labarin kuma Babbar Sallah, Gwamnatin Ganduje Ta Sallami Shugaban Makaranta Saboda Hutun Sallah

Gwamnatin Kano ta sallami shugaban makarantar sakandiren gwamnati dake Ɗanbatta.

Wannan hukucin ya biyo bayan bada hutun sallah da shugaban yayi ga ɗaliban ajin ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262