Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jiha a Gidanta

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jiha a Gidanta

  • Yan bindiga sun ce mahaifiyar sakataren gwamnatin jihar Bayelsa
  • An sace Madam Betinah Benson ne a gidanta misalin karfe 11 na dare
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da lamarin tana mai cewa an fara farautar yan bindigan

Wasu Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mahaifiyar sakataren gwamnatin jihar Bayelsa, Mrs Betinah Benson.

The Punch ta ruwaito cewa wadanda suka sace ta sun taho ne sanye da kaki irin ta sojoji.

An gano cewa an sace mahaifiyar Konbowei Benson a daren ranar Talata a gidansa da ke tsohuwar rukunin gidajen assembly ta Yenagoa.

DUBA WANNAN: Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO da Buhari ya naɗa

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar SSG Na Jihar Bayelsa
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar SSG Na Jihar Bayelsa
Asali: Original

DUBA WANNAN: Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

Dan ta, kafin Gwamna Douye Diri ya nada shi a matsayin sakataren gwamnatin jihar Bayelsa a Fabrairun 2020, ya rike mukamin kakakin majalisar dokokin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah

Kazalika, shine mai neman takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a 2019 a jihar.

Kawo yanzu dan siyasan bai ce komai ba game da sace mahaifiyarsa.

Yan sanda sun bazama neman yan bindigan

Rundunar yan sandan jihar ta Bayelsa ta tabbatar da sace Madam Betinah Benson.

Kakakin yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a Yenagoa a ranar Laraba, yana mai cewa tuni an fara farautar bata garin.

Kakakin yan sandan ya ce:

"Rundunar yan sandan Bayelsa ta fara farautar wadanda suka sace Madam Betinah Benson don kama su da ceto ta.
"An sace Madam Betinah Benson, mai shekaru 80, ne a ranar 20 ga watan Yulin 2021 misalin karfe 11 na dare a gidanta da ke tsohuwar rukunin gidajen yan majalisa, Azikoro Road, Yenagoa.
"Masu garkuwar sun afka gidan ta sanya da kakin sojoji suka tafi da ita wani wuri da ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

"Kwamishinan yan sandan jihar Bayelsa, CP Mike Okoli fsi da wasu jami'an tsaro sun ziyarci inda abin ya faru. An fara bincike."

Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Takwas a Jirgin Ruwa

A wani labarin daban, a kalla mutane takwas da ke tafiya a jirgin ruwa mai daukan fasinjoji ne aka sace a kan hanyar Kula-Abonrma a jihar Rivers kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wasu da ake zargin yan fashin jirgin ruwa ne suka sace matafiyan a ranar Litinin da safe, a cewar shugaban kungiyar ma'aikatan jiragen ruwa ta Nigeria (MWUN) Jonah Jumbo.

Jumbo ya ce cikin mutanen takwas da aka sace, biyar mambobin kungiyar MWUN ne a Kula, karamar hukumar Akuku-Toro da ke hanyarsu na zuwa Fatakwal domin hallartar taro a cewar rahoton na The Nation.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel