Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO da Buhari ya naɗa

Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO da Buhari ya naɗa

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi matsayin sabon shugaban hukumar NECO
  • Sanarwar nadin na dauke ni ciki wata wasika mai dauke da sa hannun ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu
  • Kafin nadinsa, Farfesa Wushishi ya yi aiki a jami'o'i da dama da suka hada da FUT Minna, Jami'ar Usman Danfodio Sokoto da sauransu

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarrabawar kasa ta NECO, Daily Trust ta ruwaito.

Mukadashin shugaba ne ya ke rike da hukumar tun bayan rasuwar tsohon shugabanta Farfesa Godswill Okeke.

KU KARANTA: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO da Buhari ya naɗa
Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO da Buhari ya naɗa. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

Obioma ya rasu ne a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen mutum 13 da Buhari ya tura majalisa ta tantance amma aka yi watsi dasu

Wata wasika mai kwana wata 16 ga wata Yulin 2021 dauke da lamba FME/PSE/NECO/1078/C.1/36 da sanya hannun ministan Ilimi, Adamu Adamu, ta ce an nada shi ne karo na farko na shekaru biyar daga ranar 12 ga watan Yulin 2021.

Ga wasu muhimman abubuwa game da sabon shugaban na NECO:

  1. An haife shi ne a ranar 5 ga watan Afrilun 1965
  2. Ya fito ne daga karamar hukumar Wushishi ta jihar Niger
  3. Farfesa ne a bangaren koyar da ilimin kimiyya
  4. Shi malami ne a tsangayar koyar da ilimi a jami'ar Usmanu DanFodio, Sokoto kafin ya koma Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna.
  5. Ya rike mukamai da dama a bagaren ilimi da suka hada da shugaban tsangayar Ilimi, FUT, Minna, shugaban tsangayar Ilimi a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai da sauransu.
  6. Yana da matar aure da yara.

'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'

Kara karanta wannan

IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu

A wani labarin daban, kun ji cewa manhajar aika saƙon kar ta kwana na WhatsApp mallakar kamfanin Facebook ta sanar da fara wani gwaji da zai bawa masu amfani da manhajar daman amfani da ita ko da wayarsu na kashe, The Punch ta ruwaito.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Injiniyoyi a Facebook sun ce sabon tsarin zai bawa mutane daman amfani da WhatsApp a wasu na'urorinsu ba tare da sun sada na'urar da wayarsu ta salula ba.

Tunda aka samar da shi a 2009, Facebook ta siya manhajar aika sakonnin a wayoyin zamani, WhatsApp, wanda ke da biliyoyin masu amfani da shi a faɗin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel