Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Takwas a Jirgin Ruwa

Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Takwas a Jirgin Ruwa

  • Yan fashin jirgin ruwa sun yi garkuwa da fasinjoji takwas a jihar Rivers
  • Biyar daga cikin fasinjojin mambobin kungiyar ma'aikatan jiragen ruwa ne
  • Kungiyar ma'aikatan jiragen ruwan ta yi kira ga jami'an tsaro su kai musu dauki

A kalla mutane takwas da ke tafiya a jirgin ruwa mai daukan fasinjoji ne aka sace a kan hanyar Kula-Abonrma a jihar Rivers kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wasu da ake zargin yan fashin jirgin ruwa ne suka sace matafiyan a ranar Litinin da safe, a cewar shugaban kungiyar ma'aikatan jiragen ruwa ta Nigeria (MWUN) Jonah Jumbo.

Da Ɗuminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji Takwas a Jirgin Ruwa
Taswirar jihar Rivers. Hoto: The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

Jumbo ya ce cikin mutanen takwas da aka sace, biyar mambobin kungiyar MWUN ne a Kula, karamar hukumar Akuku-Toro da ke hanyarsu na zuwa Fatakwal domin hallartar taro a cewar rahoton na The Nation.

Kara karanta wannan

Badaru Ya Buƙaci Musulmi Su Yi Addu’a Domin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Ya yi kira ga wadanda suka sace su da su gaggauta sakinsu yana mai kira ga gwamnatin jihar da jami'an tsaro su dauki mataki.

KU KARANTA: Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah

Ya ce:

"Kungiyar MWUN ta kira mambobinta na Kula da Abomema taro a ofishin jiha da ke Fatakwal a safiyar yau Litinin.
"An kan hanyarsu daga Kula, mun samu rahoto cewa an yi garkuwa da jami'an mu da za su tafi taron.
"An yi garkuwa da dukkan fasinjojin, ciki har da wasu mutane uku da ke jirgin. Har yanzu babu wanda ya ji wani abu daga wadanda suka sace su.
"Don haka muna kira ga al'umma, gwamnati da jami'an tsaro su taimaka mana suka yadda za a tuntubi masu garkuwar."

Mai magana da yawun yan sandan jihar Nnamdi Omoni ya ce ba a riga an yi masa bayani kan afkuwar lamarin ba.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

A wani labarin mai kama da wannan, yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mata tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel