Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane da Dama a Kauyukan Jihar Benuwai

Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane da Dama a Kauyukan Jihar Benuwai

  • Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayuwarsu a ƙauyuka daban-daban na jihar Benuwai
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutanen ne a ƙauyuka uku dake ƙaramar hukumar Guma
  • Shugaban ƙaramar hukumar ya koka kan harin wanda ake zargin makiyaya da aikatawa

Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayuwarsu a wasu ƙauyukan dake ƙaramar hukumar Guma, jihar Benuwai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Wani shaida ya bayyana cewa an aikata kisan ne a wurare daban-daban ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Guma, harda masu bada agajin gaggawa biyu.

Shugaban ƙaramar hukumar Guma, Caleb Aba, ya shaidawa manema labarai a Makurdi, ta wayar salula, cewa:

"An kashe mutum 4 a ƙauyen Mbabai, da wasu uku a yankin Uzurov yayin da aka kashe mutum ɗaya a ƙauyen Uvir duk ƙarƙashin ƙaramar hukumar Guma."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

An kashe mutum 10 a Benuwai
Matsalar Tsaro: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane da Dama a Kauyukan Jihar Benuwai Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Ana zargin fulani makiyaya

Aba wanda ya ɗora alhakin kashe-kashen kan fulani makiyaya, ya nuna rashin jin dadinsa kan lamarin saboda babu wata rashin jituwa tsakanin mutanen yankunan da makiyayan.

Ya ƙara da cewa mutum uku da aka kashe a ƙauyen Nzorov, waɗanda suka haɗa da ma'aikatan jin kai biyu, jami'an operation OPWS sun dauke gawarwakinsu.

Wasu mazauna yankin, sun bayyana cewa sai da maharan suka sace masu aikin bada agajin kafin daga bisani su kashe su.

An kashe makiyaya biyu

A ɗaya ɓangaren kuma, sakataren ƙungiyar fulani miyetti Allah (MACBAN), Ibrahim Galma, yace an kashe fulani makiyaya biyu a iyakar dake tsakanin jihar Nasarawa da Benuwai.

Galma wanda ya musanta hannun fulani a kashe mutum takwas a Gulma, ya bayyana cewa ya samu labarin kashe makiyaya biyu a iyaka daga jihar Nasarawa.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga da Dama Yayin Wani Artabu a Neja

Kakakin hukumar yan sandan jihar Benuwai, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.

"An kai hari kan wasu mutum uku kuma an kashe su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona a Tomanyiin, ƙaramar hukumar Guma." inji Anene.

A wani labarin kuma Cutar COVID19: NAFDAC Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ba Ta Amince da Magungunan Gargajiya Ba

Hukumar NAFDAC tace har yanzun ba'a gano wani magani ba da yake maganin cutar COVID19.

Shugabar NAFDAC tace babu wani maganin gargajiya da hukumar ta amince da shi a yanzun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262