Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Neman Kafa Kasar Yarbawa Za Su Yi Zanga-Zanga Kan Tsare Igboho a Kotonou

Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Neman Kafa Kasar Yarbawa Za Su Yi Zanga-Zanga Kan Tsare Igboho a Kotonou

  • Masu fafutikan kafa kasar Yarbawa za su yi zanga-zanga lumana don neman a sako Sunday Igboho
  • Sanarwar da mai magana da yawun Igboho ya fitar ta ce za su hadu a gidan Igboho misalin karfe 12 na ranar Alhamis
  • A ranar Litinin ne jami'an tsaro suka kama Sunday Igboho da matarsa Ropo a hanyarsu na neman zuwa kasar Jamus

Masu neman ballewa daga Nigeria domin kafa kasar Yarbawa suna shirin yin zanga-zanga saboda tsare daya daga cikin jagoran tafiyarsa Cif Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, The Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a dandalin sada zumunta ta Facebook a cewar rahoton na The Punch.

Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Neman Kafa Kasar Yarbawa Za Su Yi Zanga-Zanga Kan Tsare Igboho a Kotonou
Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Neman Kafa Kasar Yarbawa Za Su Yi Zanga-Zanga Kan Tsare Igboho a Kotonou
Asali: Original

DUBA WANNAN: Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah

Sanarwar ta ce:

"Sanarwar, Sanarwar, Sanarwar, muna rokon dukkan yan gwagwarmaya su hadu a gidan Cif Sunday Igboho domin yin zanga-zangar lumana domin nuna wa duniya ko shi wane irin mutum ne a matsayin daya daga cikin dalilan sakinsa, don Allah mu hadu a gidansa a Soka, a Ibadan kafin karfe 12 na rana a yau. Mun gode Allah ya yi albarka. Kasar Yarbawa yanzu yanzu!"

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

Idan za a iya tunawa, an kama Igboho da matarsa, Ropo a filin tashin jirage na Cadjèhoun a Kotonou, Jamhuriyar Nijar misalin karfe 8 a daren ranar Litinin. Daga bisani an tsare su a wurare daban.

Tuni dai gwamnatin Nigeria ta fara kokarin ganin yadda za a dawo da su Abuja amma kungiyoyi da dama da mutane sun soki hakan.

KU KARANTA: Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO da Buhari ya naɗa

Igboho, wanda ya yi fice bayan ya bawa makiyaya wa'adin barin yankin kudu maso yamma ya tsere daga gidansa ne yayin da jami'an tsaro suka kai samame, daga nan kuma aka ayyana nemansa ruwa a jallo.

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

A wani labarin mai alaka da wannan, babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Shugaban lauyoyin, Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da The Punch a daren ranar Talata.

Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164