NAF: Rundunar sojin sama ta magantu kan labarin sabon hatsarin jirgin sama a Kaduna
- Rundunar sojin sama ta Najeriya ta karyata rahotanni dake cewa jirgin samanta ya yi hatsari a Kaduna
- Kakakin rundunar sojin, Edward Gabkwet ya ce babu hatsarin da aka yi amma yana jiran rahotanni daga sauran garuruwa
- A jiya ne rahotannin sabon hatsarin da jirgin NAF wanda ya taso daga jihar Adamawa ya karade kafafen sada zumunta
NAF
Rundunar sojin saman Najeriya, NAF, ta musanta rahotannin dake yawo na hatsarin da jrigin samanta ya kara yi a Kaduna a ranar Lahadi da ta gabata.
Akwai rahotannin dake yawo na cewa jirgin sojojin saman Najeriya wanda ya taso daga jihar Adamawa ya fadi a wani wuri a cikin jihar Kaduna.
NAF tana jiran rahotanni
Amma kuma yayin da aka tuntubi mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet, ya sanar da TheCable cewa babu wani hatsari da ya auku a Kaduna kamar yadda ya sanar da manema labarai.
KU KARANTA: Da duminsa: Soludo ya magantu kan tsame sunansa daga na 'yan takara a Anambra
KU KARANTA: Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1
Amma kuma ya kara da cewa yana jiran labarai daga sauran wurare a lokacin rubuta wannan rahoton, The Guardian ta ruwaito.
Wannan cigaban na zuwa ne bayan watanni da aka yi mummunan hatsarin sama da ya yi sanadin mutuwar Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasan Najeriya,
Baya ga Attahiru, hatsarin da ya auku a kusa da filin jirgin sama na Kaduna yayi sanadin mutuwar wasu zakakuran sojoji goma na rundunar.
Hedkwatar tsaro tace hatsarin da jirgin saman sojoji Beechcraft 350 ya faru ne sakamakon yanayin gari maras kyau.
"Mummunan lamarin ya auku ne bayan jirgin ya sauka a filin jiragen sama na Kaduna saboda yanayin gari mara kyau," Onyeama Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin kasa yace a waya takarda.
“Shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor ya bada umarnin binciken lamarin da kuma abinda ya kawo mummunan hatsarin."
A wani labari na daban, wani jigo a jam'iyyar APC, Dr Sani Abdullahi Shinkafi yayi kira ga jam'iyyar da kuma sifeta janar na 'yan sandan Najeriya da su bada umarnin gaggauta tarwatsa sashin Abdulaziz Yari na APC a jihar Zamfara.
A wani korafi da aka mika ga sifeta janar na 'yan sandan Najeriya mai kwanan wata 15 ga Yuli, Shinkafi yace Yari da magoya bayansa suna kirkiro tashin hankali a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
"Bayan sauya shekar da zababben gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad da ni muka yi daga jam'iyyar PDP da APGA zuwa APC, Gwamna Mai Mala Buni a jihar Yobe tare da kwamitinsa sun zo sun karbemu kuma sun sanar da rushe kwamitin shugabannin jam'iyyar tun daga matakin jiha har zuwa gunduma."
Asali: Legit.ng