COVID-19: Gwamnatin Kano ta soke yin dukkan hawan sallah da shagulgula

COVID-19: Gwamnatin Kano ta soke yin dukkan hawan sallah da shagulgula

  • Gwamnatin jihar Kano ta soke dukkan hawan sallah na babbar sallah ta wannan shekarar
  • Wannan na zuwa ne bayan kwamitin fadar shugaban kasa ya saka jihar Kano cikin jihohin da cutar korona za ta iya barkewa
  • Gwamnatin jihar ta ce wannan matakin ne sassan nahiyar Afrika suka dauka sakamakon gano sabon nau'in korona a yankin

Gwamnatin jihar Kano ta soke dukkan hawan gargajiya tare da shagulgulan babbar sallah a wannan shekarar, Daily Trust ta wallafa.

Wannan matakin na zuwa ne bayan mako daya da kwamitin fadar shugaban kasa na lura da korona ya bayyana wasu jihohi shida da suka hada da Kano a cikin jihohin da za a iya samun barkewar cutar.

KU KARANTA: Akwai bayyananniyar yarjejeniya cewa Buhari zai mika mulki ga Tinubu, Sanata Hanga

COVID-19: Gwamnatin Kano ta soke yin dukkan hawan sallah da shagulgula
COVID-19: Gwamnatin Kano ta soke yin dukkan hawan sallah da shagulgula. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammadu Garba wanda ya sanar da hakan yace za a yi sallar idin babbar sallah ne a dukkan masarautu biyar da kuma masallatan dake fadin kasar.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano da wasu masarautu su soke hawan sallah

Ya ce wannan cigaban na daga cikin matakan da Najeriya, kamar sauran sassan nahiyar Afrika suka dauka saboda tasowar annobar korona a karo na uku bayan gano sabon nau'in cutar.

Garba ya ce halin ko-ta- kwanan da hukumomi suka sanar na wasu jihohi yasa aka hana shagalin sallah da kuma taro. Ya ce ba za a yi hawan sallah ba wanda akan yi kan dawaki ana zagaya cikin gari cikin tarukan jama'a.

Kwamishinan yayi kira ga jama'a da su kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar cutar wanda ya hada da amfani da takunkumin fuska, wanke hannaye da kuma nesa-nesa da juna yayin sallar idi.

Hakazalika, masarautar Kano ta hannun sakatarenta, Abba Yusuf, ya tabbatarwa da Daily Trust cewa ba za a yi hawan sallah ba a wannan shekarar.

A wani labari na daban, Sanata Rufai Hanga jigo ne na jam'iyyar APC kuma shine wanda ya kirkiro tsohuwar jam'iyyar CPC wacce ta hade da ACN, wani sashi na PDP da APGA wurin kafa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Cutar kwalara ta barke a Abuja, mutane 604 sun kamu, 54 sun riga mu gidan gaskiya

Daily Trust ta tattauna da Sanata Hanga wanda tsohon dan majalisar wakilai ne kuma ya wakilci Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.

Tsohon sanatan ya bayyana alakarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma alkawarin dake tsakanin yankin arewa da kudu kafin hawa mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel