Cutar COVID19: NAFDAC Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ba Ta Amince da Magungunan Gargajiya Ba

Cutar COVID19: NAFDAC Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ba Ta Amince da Magungunan Gargajiya Ba

  • Hukumar NAFDAC tace har yanzun ba'a gano wani magani ba da yake maganin cutar COVID19
  • Shugabar NAFDAC tace babu wani maganin gargajiya da hukumar ta amince da shi a yanzun
  • Ta gargaɗi yan Najeriya game da yawan amfani da tafarnuwa da kuma albasa

Hukumar kula da inganci abinci da magunguna (NAFDAC) ta bayyana dalilin da yasa har yanzun ba ta amince maganin gargajiya ba wajen yaƙi da cutar COVID19, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ga Yan Najeriya

Leadership ta ruwaito cewa, NAFDAC ta gargaɗi masu bincike da masu bada maganin gargajiya kan su guji baiwa mutane magungunansu da sunan maganin cutar COVID19.

Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, itace ta faɗi haka a wani jawabi da ta fitar da hannun kakakin hukumar, Sayo Akintola, ranar Lahadi.

Ta bayyana cewa NAFDAC ba ta amince da wani maganin gargajiya ba har zuwa yanzun a dukkan faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

Hukumar NAFDAC
Cutar COVID19: NAFDAC Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ba Ta Amince da Magungunan Gargajiya Ba Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shugabar tace har yanzun babu wani magani ɗaya da aka gano wanda zai magance cutar COVID19 kai tsaye.

Tace: "Ba tare da tabbatarwa daga NAFDAC ba, babu wanda zai yi ikirarin cewa samfurin maganinsa yana maganin COVID19. Tabbas wasu suna amfani da irinsu kuma suna samun sauki."

"Amma ba tare da amincewar masu binciken kimiyya ba , ba zamu taba amincewa mutane su sha wani maganin gargajiya ba da sunan maganin korona."

NAFDAC ta yi gargaɗi kan cin tafarnuwa da albasa

Farfesa Adeyeye ta gargaɗi yan Najeriya a kan cin albasa da tafarnuwa da tunanin za su magance musu cutar korona.

"Idan kaci albasa ko tafarnuwa sosai, mutane zasu fara gudunka ne domin kana warin waɗannan abubuwan," inji ta.

Sai dai ta jaddada cewa Tafarnuwa da Albasa da sauran kayan itatuwa suna ƙara wa jikin mutum ƙarfi da lafiya.

KARANTA ANAN: Gwamna Ya Caccaki Sanatocin APC, Ya Fadi Munafuncin da Suke Shiryawa a Zaben 2023

Kara karanta wannan

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

Tace: "Ko da kana cin su, ya kamata ka kare kanka, idan kaci albasa da tafarnuwa amma baka sanya takunkumin baki ba zaka kamu da korona."

"Idan kana muhalli mara tsafta kuma baka wanke hannu akai-akai, zaka iya kamuwa da cutar korona, sabida haka ya kamata a sanya komai a inda ya dace."

A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga da Dama Yayin Wani Artabu a Neja

Gwarazan yan sanda a jihar Neja sun hallaka yan bindiga akalla 10 a wani gumurzu da suka yi.

An fafata tsakanin yan sandan da maharan, inda suka samu nasarar fatattakar su daga kai hari ƙauyen Kundu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262