Yan Bindiga Sun Sako Sarki Mai Daraja Ta Daya da Suka Sace a Kogi

Yan Bindiga Sun Sako Sarki Mai Daraja Ta Daya da Suka Sace a Kogi

  • Yan bingida sun sako sarkin da suka sace a jihar Kogi, bayan shafe kwanaki biyar a hannun su
  • Wata majiya dake kusa da fadar basaraken ta bayyana cewa an sako shi da yammacin Asabar
  • Maharan sun yi awon gaba da sarkin ne yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga Okene

Sarki mai daraja ta ɗaya a Kogi, Adogu na Eganyi wanda yan bindiga suka sace kwanaki biyar da suka gabata ya kuɓuta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga da Dama Yayin Wani Artabu a Neja

Wata majiya dake kusa da fadar sarkin ta haƙaito sarkin na bayani bayan kuɓutarsa, inda yace: "Bayan doguwar tafiya a cikin daji, waɗanda suka sace ni sun dawo da ni Ebiraland da yammacin Asabar."

Yan Bindiga sun sako basaraken Kogi
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sako Sarki Mai Daraja Ta Daya da Suka Sace a Kogi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Majiya ta ƙara da cewa basaraken ba zai iya bayyana ainihin inda suka kai shi ba amma yana da tabbacin an fitar da shi daga yankin Ebiraland, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga da Dama Yayin Wani Artabu a Neja

Ba bu tabbas ko an biya kuɗin fnasa

Hakazalika, majiyar tace ba bu tabbacin an biya kuɗin fansa domin sakin basaraken ko ba'a biya ba, amma dai yan bindigan sun nemi a basu naira miliyan N30m da farko.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Jagoran Yan Bindiga, Turji, Ya Sako Daruruwan Mutanen da Ya Sace a Zamfara

Wasu mutane ɗauke da makamai sun yi awon gaba da basaraken ne ranar Talata a kan hanyar Okene–Ajaokuta yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya halarci wani taro a Okene.

A wani labarin kuma Sanata Ahmad Lawan Ya Faɗi Dalilin da Yasa Sanatocin APC Suka Yi Fatali da Dokar Tura Sakamakon Zaɓe Ta Na'ura

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, yace ba yadda za'ai Najeriya ta canza zuwa tura sakamakon zaɓe ta Na'ura kai tsaye.

Hukumar NCC tace kashi 50% na sassan Najeriya kacal zasu iya aika saƙon sakamako ta na'ura ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jagoran Yan Bindiga, Turji, Ya Sako Dukan Mutanen da Ya Sace, Bisa Sharadi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262