Babu aikin da APC tayi da ta cancanci cigaba da mulki a 2023, Hanga

Babu aikin da APC tayi da ta cancanci cigaba da mulki a 2023, Hanga

  • Sanata Rufai Hanga Jigo ne a jam'iyyar APC kuma shi ya kirkiro tsohuwar jam'iyyar CPC
  • Sanatan ya koka da yadda mulkin APC ke tafiya inda yace basu cancanci cin zabe ba a 2023
  • Hanga yace babu shakka gyaran dokokin zaben da ake yi duk shirin magudi ne a shekarar 2023

Sanata Rufai Hanga jigo ne na jam'iyyar APC kuma shine wanda ya kirkiro tsohuwar jam'iyyar CPC wacce ta hade da ACN, wani sashi na PDP da APGA wurin kafa jam'iyyar APC.

Daily Trust ta tattauna da Sanata Hanga wanda tsohon dan majalisar wakilai ne kuma ya wakilci Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.

Tsohon sanatan ya bayyana alakarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma alkawarin dake tsakanin yankin arewa da kudu kafin hawa mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari

Kara karanta wannan

2023: Cancanta za mu duba wajen zabar Shugaban kasa, kungiya ta bayyana zabinta

Babu aikin da APC tayi da ta cancanci cigaba da mulki a 2023, Hanga
Babu aikin da APC tayi da ta cancanci cigaba da mulki a 2023, Hanga. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Daular duniya: Bidiyoyin lefen alfarma na Zarah Bayero daga Iyalin Shugaba Buhari

A yayin da aka bukaci jin ta bakin Sanata Hanga ko zai yuwu jam'iyyar APC ta cigaba da mulki a shekarar 2023, sanatan yace ita kanta jam'iyyar a tarwatse take kuma ta san bata cancanci cigaba da mulki ba.

"APC ta san a tarwatse take. Sun san cewa babu abinda suka yi a ko ina da suka cancanci a sake zabensu. Amma kuma sun yi kunnen kashi, suna kokarin yin magudi ne.

"Ba a yin magudi a ranar zabe. Ana shirya shi ne kafin lokacin. Wannan gyaran dokokin zaben shine magudi. Ina da gogewa. Wannnan gyaran dokokin zaben yana share musu hanya ne ta yadda zasu yi magudin.

"Na taba zama dan majalisar wakilai. Akwai wani lokaci da ake sako wani abu a cikin dokokin zabe. Mu muka fitar da dokokin zaben da yanzu Najeriya ke son ta gyara. Ina daga cikin mambobin da muka yi wadannan dokokin kalma bayan kalma. Akwai abinda suke son karawa domin amfanin kansu," Hanga yace.

Kara karanta wannan

2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu

A wani labari na daban, jami'an hukumar 'yan sanda sun sheke shugaban wata kungiyar garkuwa da mutane mai suna Abdullahi Bummi a jihar Jigawa.

An kashe dan ta'addan ne yayin wani samamen da aka kai sansanin 'yan bindigan dake Gallu, karamar hukumar Yankwashi ta jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'an 'yan sanda sun ceto wata tsohuwa mai shekaru 65 yayin samamen wanda aka yi shi na hadin guiwa tsakanin 'yan sandan Katsina da na Jigawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng