Akwai bayyananniyar yarjejeniya cewa Buhari zai mika mulki ga Tinubu, Sanata Hanga

Akwai bayyananniyar yarjejeniya cewa Buhari zai mika mulki ga Tinubu, Sanata Hanga

  • Tsohon dan majalisar wakilai, Sanata Rufai Hanga ya tabbatar da cewa akwai yarjejeniya tsakanin Buhari da Tinubu
  • Hanga yace tabbas an yi bayyananniyar yarjejeniya wacce da yawa an sani kan baiwa Tinubu mulki a 2023
  • Jigon jam'iyyar APC ya ce wannan yarjejeniyar ce tasa Bola Tinubu ya cigaba da zama a jam'iyyar duk da ba a yi da shi

Wanda ya kirkiro tsohuwar jam'iyyar CPC, Sanata Rufai Hanga, ya ce akwai bayyanannen yarjejeniya cewa Buhari zai mika mulki hannun shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu a 2023.

Hanga wanda ke shugabantar daya daga cikin tsoffin jam'iyyun da suka hade suka zama APC a 2014 ya sanar da hakan a wata tattaunawa da Daily Trust inda yayin bayanin cewa wannan yarjejeniyar ce dalilin da yasa Tinubu yake APC bayan kammala wa'adin Buhari na farko.

KU KARANTA: Daular duniya: Bidiyoyin lefen alfarma na Zarah Bayero daga Iyalin Shugaba Buhari

Kara karanta wannan

Ku tarwatsa bangaren Yari na APC a Zamfara, Shinkafi yayi kira ga Buni da IGP

Akwai bayyananniyar yarjejeniya cewa Buhari zai mika mulki ga Tinubu, Sanata Hanga
Akwai bayyananniyar yarjejeniya cewa Buhari zai mika mulki ga Tinubu, Sanata Hanga. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1

"Wannan bayanannen sirri ne. Akwai yarjejeniya kuma a bayyane. Sun yi yarjejeniyar cewa Tinubu zai karba mulki, Hakan ce ta sa bai bar jam'iyyar ba tun a karon farko na mulkin Buhari. Da a ce Tinubu ya san ba zai samu komai ba, da ya zare jikinsa tun mulkin karon farko. Amma ya san akwai yarjejeniya," yace.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Hanga ya nuna tantamarsa na cewa ko jam'iyyar APC za ta baiwa Tinubu tikitinta, lamarin da yace zai iya kawo hargitsi da kishin neman mulki daga wasu gwamnoni da makusantan shugaban kasan.

Tsohon dan majalisar ya ce duk da manyan jam'iyyu biyun suna da nasu matsalolin, zai yuwu 'yan Najeriya su koma bayan PDP sakamakon rashin kwazon da jam'iyyar APC ta nuna karkashin mulkin shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1

A wani labari na daban, wani jigo a jam'iyyar APC, Dr Sani Abdullahi Shinkafi yayi kira ga jam'iyyar da kuma sifeta janar na 'yan sandan Najeriya da su bada umarnin gaggauta tarwatsa sashin Abdulaziz Yari na APC a jihar Zamfara.

A wani korafi da aka mika ga sifeta janar na 'yan sandan Najeriya mai kwanan wata 15 ga Yuli, Shinkafi yace Yari da magoya bayansa suna kirkiro tashin hankali a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan sauya shekar da zababben gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad da ni muka yi daga jam'iyyar PDP da APGA zuwa APC, Gwamna Mai Mala Buni a jihar Yobe tare da kwamitinsa sun zo sun karbemu kuma sun sanar da rushe kwamitin shugabannin jam'iyyar tun daga matakin jiha har zuwa guunduma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng