Gwamna Bello Matawalle: Arewa ita ce matsalar kanta da kanta
- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara yace 'yan arewa sune babbar matsalar kansu da kansu
- Matawalle ya musanta labarin dake yawo na cewa ya sauya sheka ne saboda ya samu damar zarcewa
- Gwamnan yace duk wata barazana ta tsohuwar jam'iyyarsa ba za ta tsorata shi ba kuma har yau shine gwamnan Zamfara
Gusau, Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce arewa ita ce matsalar kanta da kanta, Daily Trust ta wallafa.
A wata tattaunawa da yayi da DW Hausa a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, Matawalle ya caccaki masu kira da a tsige shi saboda sauya jam'iyya da yayi.
KU KARANTA: Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1
KU KARANTA: Ku tarwatsa bangaren Yari na APC a Zamfara, Shinkafi yayi kira ga Buni da IGP
Ba saboda zarcewa na sauya sheka ba
Gwamnan ya musanta rade-radin dake yawo na cewa ya koma jam'iyyar APC ne saboda yana son zarcewa mulkin jihar a karo na biyu, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan PDP ya caccaki majalisar dattawa, ya ce mika ikon INEC ga NCC ya saba wa kundin tsarin mulki
"Kamata yayi jama'ar jihar Zamfara su cigaba da harkokinsu kamar baya. Wadanda ke yada hakan duk rashin sani ne. Sune suka damu da mulki karo na biyu ba ni ba."
“Babu wanda ke da tabbacin ganin gobe, kai sa'a daya nan gaba babu tabbaci. Ina da wadatar zuci kan abinda Allah yayi min. Abinda na sani shine, ko da wannan wa'adin mulkin na kammala cikin nasara, toh ina godiya ga Allah da kuma jama'ar Zamfara."
Ba zan firgita da barazanar PDP ba
A bangaren kokarin jam'iyyar PDP na kwace kujerarsa, Matawalle ya ce: "Ba ni bane gwamna na farko da ya sauya sheka yana kan mulki ba. Amma abinda za ku gane a nan shine, mu 'yan arewa mune matsalar kanmu da kanmu. Hakan ce ta sa muna gani mulki zai bar yankinmu. Abinda yasa kuwa shine dukkan wadanda ke kiran kansu da shugabanni a arewa duk mayaudara ne kuma matsantawa jama'a suke.
"Dalilina a nan shine, akwai tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto da ya sha alwashin cewa idan har PDP bata kaini kotu ba, toh zai bar ta. Suna ta cewa dole a gurfanar da ni.
“Amma idan an maka ni a kotu, babu abinda zasu yi. Basu san doka bane ko kuma kundun tsarin mulkin Najeriya? Ni na fara sauya sheka? Babu abinda zai tsorata ni kuma zan cigaba da shugabancin Zamfara ko suna so, ko basu so."
A wani labari na daban, Chukwuma Soludo, daya daga cikin 'yan takarar zaben gwamnonin da za a yi a jihar Anambra na ranar shida ga watan Nuwamban shekarar nan yace har yanzu yana cikin 'yan takara.
Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta cire sunan shi daga cikin jerin 'yan takara.
A wata takarda da kungiyar yakin neman zabensa ta fitar a madadinsa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce har yanzu shine dan takarar jam'iyyar APGA, Daily Trust ta wallafa.
Asali: Legit.ng