Jirgin saman sojojin sama na Najeriya ya sake hadari a Kaduna, jami'an ceto sun kai dauki

Jirgin saman sojojin sama na Najeriya ya sake hadari a Kaduna, jami'an ceto sun kai dauki

  • Wani jirgin sojin saman Najeriya ya fadi a wani yankin jihar Kaduna yayin fatattakar 'yan bindiga
  • Rahoto ya bayyana cewa, jirgin ya taso daga jihar Adamawa ne domin ya yaki 'yan bindiga a Kaduna
  • Har yanzu dai ba a san adadin asarar da aka yi ba, amma dai ana kan bincike kan yadda lamarin yake

Babu wani labari game da halin da ma'aikatan jirgin dake cikin jirgin ke ciki a lokacin hada wannan rahoton.

Rahoto da muke samun ya shaida cewa, jirgin saman sojin sama na Najeriya ya yi hadari a cikin jihar Kaduna.

Jirgin mai suna AlfaJet an ce ya bar Yola babban birnin jihar Adamawa ne don ayyukan yaki da ta'addanci wanda kwatsam ya fadi a daya daga cikin kauyukan yankin jihar ta Kaduna.

KARANTA WANNAN: Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano da wasu masarautu su soke hawan sallah

Yanzu-Yanzu: Jirgin sojojin saman Najeriya ya sake hadari a Kaduna
Jirgin saman sojojin saman Najeriya | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wani babban jami’in NAF da bai so a ambaci sunansa a rubuce ba, ya fadawa jaridar Daily Sun cewa sansanin NAF din da ke Yola tuni ya shiga bakin ciki da jimami lokacin da labarin hadarin ya iso su.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

Ko da yake NAF har yanzu ba ta tabbatar da afkuwar hatsarin ba, majiyar ta ce:

“Zan iya fada muku da gaske cewa jirgin NAF AlfaJet ya fadi a Kaduna. Jirgin saman ya bar Yola ne domin yaki da 'yan ta'adda a Kaduna.
“A yanzu da muke magana, ba mu san halin da ma’aikatan jirgin ke ciki ba amma tawagar bincike sun tafi wurin da hatsarin ya faru.
"Yanzu haka sansanin sojin sama da ke Yola yana cikin halin juyayi saboda wannan hatsarin ya fara yi wa rundunar NAF yawa, hukumomi na bukatar yin wani abu koda kuwa hakan na nufin yin sihiri ne saboda wannan ba lamari ne na haka kawai ba.”

Lokacin da aka tuntubi daraktan hulda da jama'a da bayanai Air Commodore Edward Gabkwet ya yi alkawarin ba da bayani daga baya, sai dai bai fadi komai ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

A baya rundunar sojin saman Najeriya ta fuskanci hadarin jirgin sama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban hafsun sojojin Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace wasu mata da shanu masu yawa

'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace wasu mata da shanu masu yawa

'Yan bindiga sun kashe wani mutumin kauye tare da yin garkuwa da mutane 7, ciki har da mata uku a karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a kauyen Anguwar Gajere dake karkashin yankin Kutemashi na karamar hukumar, a ranar Asabar 17 ga watan Yuli.

An kuma gano cewa 'yan bindigan sun sace shanu sama da 50 daga kauyen.

Wani mazaunin yankin, Mohammed Birnin Gwari, ya shaida wa Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa ’yan bindigan sun zo ne a kan babura da misalin karfe 1 na rana.

KARANTA WANNAN: Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

A wani labarin, Akalla jami'an Kwastam uku da wani soja sun ji rauni lokacin da wasu masu fasa kwauri suka far musu a yankin Igboora da ke karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Theophilus Duniya, Jami’in Hulda da Jama’a na Kwastam, sashin Ayyuka na Tarayya, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar kuma ya ba manema labarai a Ibadan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.