Jerin sunayen mutum 13 da Buhari ya tura majalisa ta tantance amma aka yi watsi dasu
Daga hawan shugaba Buhari mulki a shekarar 2015 zuwa yanzu, ya tura mutane 13 majalisa amma ta ki amincewa dasu. Ta kowace fuska, majalisar ta dattawa na da dalilai kwarara na kin amincewa da nadin wadannan mutane.
Tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2015, ya tura sunayen mutane da yawa ga Majalisar Dattawa don tabbatar da nadinsu.
Duk da yake an tabbatar da yawancin wadanda aka zaba, wasu kalilan kuma an ki amincewa da su bisa dalilai daban-daban.
Na baya-bayan nan ita ce Lauretta Onochie, mai taimakawa shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai.
KARANTA WANNAN: Jirgin saman sojojin sama na Najeriya ya sake hadari a Kaduna, jami'an ceto sun kai dauki
Daily Trust a ranar Lahadi ta bayyana sunayen mutane 13 daga cikin wadanda majalisar ta dattajai ta ki amincewa da su a cikin shekaru shida na gwamnatin Buhari.
Legit.ng Hausa ta tattaro sunayen mutanen kamar haka:
- Olatokunbo Ajasin
- Donatus Eyinnah
- Igo Weli
- Ezekiel Yisa Benjamin
- Aliyu Saidu Abubakar
- Justice Sylvanus Nsofor
- Daodu Igbekele Jacob
- Dr Joy Nunieh
- Ibrahim Magu
- Raheem Muedeen Olalekan
- Nnamdi Anyaechie
- Lauretta Onochie
Majalisar dattijai ta ki amince da dukkan wadannan mutanen da shugaba Buhari ya tura domin tantance saboda wasu dalilai da majalisar ta lura dasu.
Jega Ya Buƙaci Sanatoci Kada Su Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Ta Naɗin Onochie
Tsohon shugaban hukumar zaɓe, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira ga majalisar dattijai kada ta amince da naɗin Lauretta Onochie, a matsayin kwamishinan INEC, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
The cable ta rahoto cewa Onochie, wacce take cikin waɗanda shugaba Buhari ya aike da sunansu, tana daga cikin waɗanda sanatocin suka tantance ranar Alhamis.
Naɗin Onochie ya jawo cece-kuce daga ƙungiyoyi masu zaman kansu, yan majalisun jam'iyyun adawa da ma wasu yan jam'iyya mai mulki ta APC.
KARANTA WANNAN: Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi
Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47
A wani labarin, Wani dan rajin kare hakkin dan adam, Malcolm Emokiniovo Omirhobo, ya yi barazanar maka Shugaba Muhammadu Buhari a kotu game da bayar da lasisin mallakar bindiga kirar AK-47 don kare kai.
Omirhobo a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 8 ga Yulin 2021, ya bukaci shugaban da ya amince da mallakar bindigogi ga mutane don kare kansu, iyalai da dukiyoyinsu daga harin 'yan ta'adda masu rike da muggan makamai.
Da yake magana da Daily Trust, lauyan ya ce a shirye yake ya kalubalanci shugaban a kotu kan wannan batun a cikin kwanaki masu zuwa.
Asali: Legit.ng