Babbar Sallah: Wani Gwamnan Arewa Ya Bada Umarnin Biyan Ma'aikatan Jiharsa Albashi Kafin Sallah
- Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, ya umarci ma'akatar kuɗin jihar ta biya ma'aikata albashin su kafin ranar salla
- Gwamnan ya kuma bada umarnin tura wa ma'aikata kuɗaɗen su kai tsaye maimakon bin ta hannun bankuna
- Daga ƙarshe ya yi wa ɗaukacin ma'aikatan fatan ayi bikin babbar sallah lafiya
Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, ya bada umarnin gaggawa cewa a biya ma'aikatan jihar albashinsu na watan Yuli kafin ranar sallah (Eid-el-kabir), kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Layin Dogo: Gwamnatin Tarayya Zata Dauki Ma'aikata 20,000 Aiki, Minista
Gwamnan ya bada umarnin biyan ma'aikatan dake ƙarƙashin jiha da kuma na ƙananan hukumomi albashinsu ranar Jumu'a 15 ga watan Yuli.
Kwamishinan kuɗi na jihar, Alhaji Ibrahim Muhammad Augie, shine ya faɗi haka a wani jawabi da yayi.
A biya albashi kai tsaye
Kwamishinan kudin ya ƙara da cewa gwamnan ya bada umarnin biyan ma'aikatan kai tsaye ba tare da anbi ta bankuna ba.
Yace: "Ma'aikatar kuɗi ta gama shirya wa tsaf wajen biyan ma'aikata albashin su kai tsaye maimakon bin ta hannun bankunan kasuwanci don guje wa ɓata lokaci."
"Kowa ne ma'aikaci zai samu albashinsa na watan Yuli cikin gaggawa ba tare da ɗaukar lokaci ba."
KARANTA ANAN: Jiragen Yaki 'Super Tucano' Guda 6 Sun Baro Amurka, Zasu Iso Najeriya Ba da Jimawa Ba, NAF
Gwamnan ya yi wa ɗaukacin ma'aikatan jihar Kebbi fatan ayi shagulgulan bikin babbar sallah lafiya.
A wani labarin kuma Cikakken Bayani, NAFDAC Ta Amince da Sabbin Rigakafin COVID19, Ta Faɗi Amfani da Hatsarinsu
Hukumar dake kula da ingancin magunguna da abinci, NAFDAC, ta amince da ƙarin rigakafin cutar COVID19 guda biyu da za'a yi amfani da su a Najeriya.
Rigakafin da hukumar ta amince da su sune, Moderna da Sputnik, kuma dukkan sunan amince da su wajen buƙatar gaggawa.
Asali: Legit.ng