Layin Dogo: Gwamnatin Tarayya Zata Dauki Ma'aikata 20,000 Aiki, Minista
- Gwamnatin tarayya zata ɗauki yan Najeriya aƙalla 20,000 aiki a layin dogon da ya taso daga Kaduna-Kano
- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, shine ya bayyana haka a wurin bikin ƙaddamar da aikin wanda ya gudana a Kano
- Yace ma'aikatarsa zata cigaba da aiki ba dare ba rana domin cika umarnin shugaba Buhari na zamanantar da layin dogo
Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa za'a ɗauki mutum 20,000 da zasu yi aiki a tashoshin jirgin ƙasa dake layin Kaduna-Kano, kamar yadda punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Duminsa: Rundunar Sojin Sama Ta Faɗi Ranar da Jiragen Yaki 'Super Tukano' Guda 6 Zasu Iso Daga Amurka
Amaechi ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Kano yayin bikin fara aikin layin dogo da ya taso daga Kaduna zuwa Kano.
Yace aikin layin dogon zai ƙara haɓɓaka tattalin arziƙi da walwala a tsakanin garuruwan da zaran an kammala shi.
Yace: "Wannan umarni ne kai tsaye daga shugaba Buhari cewa in tabbatar mun samar da ayyukan yi ga yan Najeriya."
"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa zamu ɗauki ma'aikata aƙalla 20,000 da zasu yi aiki a tashoshi."
Nan da wata 18 za'a kammala aikin
Ministan ya ƙara da cewa aikin, wanda aka baiws kamfanin gini na ƙasae China, za'a kammala shi cikim watanni 18.
A cewarsa, za'a samar da duk wani abu da ake buƙata a layin dogon da suka haɗa da ruwa, hasken wutar lantarki, sabin mai ƙarfi da dai sauransu.
KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: NAFDAC Ta Amince da Sabbin Rigakafin COVID19, Ta Faɗi Amfani da Hatsarinsu
"Ma'aikatar sufuri zata cigaba da aiki ba dare ba rana domin cika umarnin shugaban ƙasa na samar da komai na zamani a layukan dogo da kuma faɗaɗa aikin." Ministan ya faɗa.
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar da Wani Muhimmin Aiki Na Biliyoyin Naira Bayan Shekara 40 da Fara Shi
Shugaba Buhari zai kai ziyara jiharsa ta Katsina, inda ake tsammanin zai ƙadɗamar da wasu muhimman ayyuka.
Shugaban zai ƙaddamar da aikin ruwa na Zube Dam a Dutsinma shekara sama da 40 bayan fara shi.
Asali: Legit.ng