Mambobin APC sun farfashewa jami'in kotu baki a jihar Ogun

Mambobin APC sun farfashewa jami'in kotu baki a jihar Ogun

  • Wasu 'ya'yan jam'iyyar APC sun lakadawa jami'in kotu mugun duka a jihar Ogun wanda ya je kai sammaci
  • An gano cewa rikici ya barke a gundumar Iperu tun bayan kammala zaben fidda gwani na kansiloli
  • Daya daga cikin 'yan takarar ya kai shugaban jam'iyya, jam'iyya da hukumar zaben jihar gaban kotu

Wasu mambobin jam'iyyar APC sun ci zarafin Adetayo Odunlami, wani ma'aikacin wata babbar kotun jihar dake Ogun a ranar Talata.

Lamarin ya faru ne a yankin Iperu, garinsu Gwamna Dapo Abiodun, Daily Trust ta ruwaito hakan.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama dilan ESN/IPOB na miyagun kwayoyi, an samu kwayoyin N150m

Mambobin APC sun farfashewa jami'in kotu baki a jihar Ogun
Mambobin APC sun farfashewa jami'in kotu baki a jihar Ogun. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Luguden wuta: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 120 a dajin Sububu dake Zamfara

Daily Trust ta tattaro cewa ma'aikacin kotun ya je Iperu dake karamar hukumar Ikenne ta jihar Ogun domin bada sammaci ga wani shugaban jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Wani dan takarar kansila, Muyiwa Osularu ya maka mataimakin shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar a karamar hukumar Ikenne, Hon Efuwape Olaitan Muhammed, jam'iyyar da kuma hukumar zabe ta jihar a gaban wata babbar kotu dake Sagamu kan zargin cire sunan shi.

Osularu yace shine wanda ya ci zaben fidda gwani wanda jam'iyyar tayi a gunduma ta 5 ta Iperu a ranar 20 ga watan Mayun wannan shekarar.

Daily Trust ta gano cewa, ya zargi cewa shugabannin jam'iyyar sun cire sunansa inda suka saka na Hon. Efuwape.

Dan takarar ya bukaci kotun da ta baiwa jam'iyyar umarnin mika sunansa a matsayin dan takara na gundumar.

Amma kuma bayan da ma'aikacin kotun ya isa gundumar domin bada sammaci, sai wasu mambobin jam'iyyar da har yanzu ba a san ko su waye ba suka lakada mishi mugun duka.

An gano cewa mutumin ya ji miyagun raunika kafin mutanen garin su cece shi daga hannun fusatattun mambobin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Uwar jam'iyya ta dakatad da Rochas Okorocha daga APC

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A wani labari na daban, luguden wutan da jiragen yakin sojin saman Najeriya suka yi wa 'yan bindiga ya hada da ran wata mata tare da 'ya'yanta hudu a Sububu dake jihar Zamfara.

Majiyoyi daban-daban sun sanar da Daily Trust cewa jiragen yakin NAF sun tsinkayi dajin Sububu tsakanin kananan hukumomin Shinkafi da Maradun yayin da mugun lamarin ya faru.

Dajin Sububu shine yanzu babbar maboyar 'yan bindiga a jihar Zamfara. Daga dajin suke kaddamar da hari kan matafiya a babban titin Sokoto zuwa Gusau da kuma kauyukan jihohin Sokoto da Zamfara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel