Hukumar NBC ta umurci gidajen TV da Rediyo su daina bayar da bayani game da hare-haren 'yan bindiga

Hukumar NBC ta umurci gidajen TV da Rediyo su daina bayar da bayani game da hare-haren 'yan bindiga

  • Hukumar NBC mai kula da kafofin labarai na murya ta gargadi kafofin da su guji yada labaran ’yan ta’adda da sauran miyagu
  • Ta ce wani lokacin masu sharhi a kafofin labaran na wuce makadi da rawa wajen yin kalaman rarrabuwar kawuna
  • Hukumar ta ce galibin jaridun Najeriya na cike da kanun labarai kan batutuwan tsaro

TheCable ta rahoto hukumar Kula da KafofofIn Watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta bukaci gidajen rediyo a Najeriya da kada su bayar da cikakken bayani game da hare-haren da ‘yan bindiga da sauran masu tayar da kayar baya ke kai wa.

A wata wasika mai dauke da kwanan wata 7 ga watan Yuli dauke da sa hannun Francisca Aiyetan, Daraktan kula da sa ido ga gidajen rediyon a hukumar NBC ta umarci gidajen rediyon da talabijin cewa kada su “Yayata ayyukan assha na masu tayar da kayar baya, ’yan bindiga da na masu satar mutane” a cikin rahotanninsu.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta karyata sakin 'yan Boko Haram, ta fayyace gaskiya

Takardar mai taken: ‘Sharhin Jaridu Da Shirye-shiryen Lamuran Yau da Kullum: Bukatar Kiyayewa’, wacce take kuma dauke da sa hannu a madadin Babban Jami’in Hukumar Balarabe Ilelah.

Hukumar ta shawarci masu watsa labaran da su yi taka-tsantsan a rahotannin da suke bayar wa saboda zurfafa “bayanai da yawa” na iya haifar da illa ga kokarin da hukumomin tsaron Najeriya ke yi, riwayar Punch.

Hukumar NBC ta umurci gidajen TV da Rediyo suyi hattara
Hukumar NBC ta umurci gidajen TV da Rediyo su daina bayar da bayani game da hare-haren 'yan bindiga Hoto: NBC.com

Hukumar NBC ta ce wadansu daga cikin batutuwan da ake tattaunaWA yayin sharhin jaridun da gidajen rediyon suke yi suna tattare da "batun nuna wariyar kabilanci" wanda ke nuna fifikon "wani sashe na kasar a kan wani sashen kuma hakan yana sanya 'yan Najeriya cikin zaman zullumi".

Tace:

“Kanun labaran yawancin Jaridu a kowace rana suna cike da batutuwa kan rashin tsaro. Duk da yake bayanai kan tsaron nada muhimmanci ga 'yan Najeriya amma akwai bukatar yin taka tsantsan saboda bayanai da yawa na iya haifar da mummunar illa a kan kokarin jami'an tsaronmu da ke kan aikinsu na magance matsalar tsaron."

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

“Don haka hukumar ta umarci masu watsa labaran da su hada kai da gwamnati wajen tunkarar kalubalen tsaro ta hanyar; kada kafofin labaran su bari ana zuzuta ayyukan assha na masu tayar da kayar bayan da ’yan ta’adda da masu satar mutane da ma ’yan bindigar da dai sauransu.

NBC ta kara da cewa gidajen jarida su shawarci masharhanta ko bakin da suka gayyato su yi tsokaci a shirye-shiryensu da kada su yi kalaman farraka ’yan Najeriya da maganganun da za su haddasa rarrabuwar kawuna, a yayin sharhin da suke yi.

Tace:

Ka da a bada cikakken bayani game da matsalolin tsaro ko wadanda wannan kalubale na tsaro ya shafa domin kar a kawo cikas ga kokarin sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro."

Asali: Legit.ng

Online view pixel