Messi zai cigaba da zama a Barcelona har 2027, amma zai rasa Naira Biliyan 20 duk shekara

Messi zai cigaba da zama a Barcelona har 2027, amma zai rasa Naira Biliyan 20 duk shekara

  • Kungiyar Barcelona ta cin ma yarjejeniya da babban ‘dan wasanta Lionel Messi
  • Tauraron zai sabunta kwantiraginsa, ya zauna a kungiyar har zuwa kakar 2027
  • A baya Messi ya na karbar kusan N45bn a shekara, zai koma samun rabin haka

Barcelona ta cin ma yarjejeniya da tauraron ‘dan wasa, Lionel Messi, inda ya yarda ya cigaba da buga wa kungiyar wasa na wani tsawon lokaci.

Jaridar Marca ta Sifen ta bayyana cewa lauyoyin Lionel Messi sun kammala duba kwantiragin da aka ba shi, kuma ya yarda da tayin da aka yi masa.

Abin da da kwantiragin ya kunsa

Lionel Messi zai kara yin wasu shekaru biyar a Barcelona. Sannan kuma an rage masa rabin abin da yake samu a matsayin albashi a kowace shekara.

KU KARANTA: Tarihin da gwarzon ‘Dan wasan Barcelona Messi zai bari a kwallo

Yanzu Messi zai rika tashi da fam Euro miliyan 350 a shekara, rabin albashin da yake kai a baya.

Kara karanta wannan

Labari da dumi-dumi: Majalisa ta amince da rokon cin danyen bashin Naira Tiriliyan 4

Idan an sa hannu a wannan kwantiragin, mai so ya saye ‘dan wasan na kasar Argentina daga Barcelona, sai ya biya akalla fam Euro miliyan 350.

Marca ta ce sai da wakilan ‘yan wasan suka yi taka-tsan-tsan domin ganin ba za a samu matsala da hukumomin harajin Sifen a wannan yarjejeniya ba.

Ana fama da rashin kudi

Kungiyoyin kwallon kafa sun shiga cikin matsin lamba a ‘yan kwanakin nan. Kulobs na fama da karancin kudin shiga saboda annobar cutar COVID-19.

KU KARANTA: Man United ta saye Sancho, ta na neman 'Dan wasan Madrid

Messi
'Dan wasa Lionel Messi Hoto: bleacherreport.com
Asali: UGC

Dole ta sa Barcelona ta fara sallamar wasu ‘yan wasa domin ta rage abin da ta ke batar wa wajen biyan albashi. Hakan zai sa a iya biyan irinsu Lionel Messi.

Daga cikin ‘yan kwallon da Joan Laporta ya rabu da su yanzu akwai Trincao, Junior Firpo, Konrad de la Fuente, Jean-Clair Todibo da ‘dan wasa Carles Alena.

Kara karanta wannan

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

Ana sa ran cewa Barcelona za ta saida Philippe Coutinho, Ousmane Dembele ko kuma Antoine Griezmann domin ta samu sararin biyan sauran taurarinta.

Hakan ya kawo karshen rade-radin tashin Messi lokacin da kungiyoyin kwallo ke cikin rashin kudi. Iirin haka ne ya sa Real Madrid ta rasa Sergio Ramos.

A watan jiya Real Madrid ta bada sanarwar cewa Ramos zai tashi daga kulob din, bayan kwantiraginsa ya kare ba tare da an cin ma wata yarjejeniya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel