Man United ta saye Sancho a kan Naira Biliyan 51, ta na shirin dauke ‘Dan wasan Real Madrid

Man United ta saye Sancho a kan Naira Biliyan 51, ta na shirin dauke ‘Dan wasan Real Madrid

  • Manchester United za ta karbi Jadon Sancho daga Dortmund
  • Kungiyar Borussia Dortmund ta tabbatar da wannan cinikin
  • Akwai yiwuwar Tauraro Raphael Varane yar bar Real Madrid

A ranar Alhamis da rana ne kungiyar kwallon kafa na Manchester United ta bada sanarwar babban sayen ‘dan wasan Borussia Dortmund, Jadon Sancho.

Kungiyar ta tabbatar da cewa ciniki ya fada tsakaninta da Borussia Dortmund a shafinta na yanar gizo.

Jadon Sancho zai zo Manchester United bayan Euro 2021

Za a karkare cinikin da zarar ‘dan wasan ya yi gwajin lafiya a kungiyar Manchester United bayan ya kammala buga wasa a gasar cin kofin nahiyar Turai.

An dauki tsawon lokaci kafin a cin ma yarjejeniya tsakanin Manchester United da kungiyar kwallon kafa na kasar Jamus a kan ‘dan wasan na Ingila.

KU KARANTA: Kungiyar Real Madrid ta zabi Anceloti ya zama sabon Kocinta

Manchester United ta ce ta biya Borussia Dortmund Dala fam miliyan 101 watau miliyan £73 kafin a sallama mata ‘dan wasan kwallon gaban mai shekaru 21.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, ‘dan wasan ya tashi a kan N51bn.

Borussia Dortmund ta tabbatar da cinikin

Goal.com ta ce Kungiyar Borussia Dortmund ta fitar da jawabi a ranar Alhamis cewa:

“’Dan wasa Jadon Sancho ya na shirin tashi daga Borussia Dortmund GmbH & Co. KGaA zuwa kungiyar Manchester United Football Club Limited.”
“Kungiyoyin biyu da kuma ‘dan wasan sun cin ma yarjejeniya a yau. Idan an kammala cinikin, Manchester United za ta biya BVB fam EUR 85.0.”

KU KARANTA: Sergio Ramos ya bar kungiyar Real Madrid

Jadon Sancho
Jadon Sancho zai tafi Ingila Hoto: www.goal.com
Asali: UGC

BVB ta ce za a karkare abubuwan da suka rage na gwajin lafiya da jarrabbawa kamar yadda FIFA ta tanada.

Manchester United ta dage a kan sayen Varane

Haka zalika Sky Sports ta ce Manchester United ta na neman ‘dan wasan bayan kungiyar Real Madrid, Raphael Varane, amma har yanzu ba a tsaida magana ba.

Varane mai shekara 28 ya yi shekaru 10 a Madrid, ya buga wa kungiyar wasanni fiye da 350.

A karshen kakar bana ne kwantiragin 'dan wasan bayan nan, Sergio Ramos ya kare da kungiyar Real Madrid. Dole ya bar kulob din bayan an ki kara masa wa'adi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel