Bayan tsawon shekaru 16, Sergio Ramos zai tattara kayansa, ya bar kungiyar Real Madrid

Bayan tsawon shekaru 16, Sergio Ramos zai tattara kayansa, ya bar kungiyar Real Madrid

  • A jiya ne kwantiragin Sergio Ramos ya kare da kungiyar Real Madrid
  • Real Madrid da ‘dan wasan ba su amince a kan sabunta kwangilarsa ba
  • Tauraron bayan zai tashi daga kungiyar da ya yi shekara 16 yana wasa

Sanarwar ban kwana da kulob

Kungiyar Real Madrid ta bada sanarwar cewa Sergio Ramos zai tashi daga kulob din. Sanarwar ta fito ne a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni, 2021.

Ga abin da sanarwar da ta fito daga shafin yanar gizon kungiyar take cewa:

“Za a kira taron manema labarai a ranar Alhamis, inda za a sanar da tashin kyaftin din Real Madrid bayan shekaru 16.”

KU KARANTA: Ramos ba zai daga La-liga ba, Atletico ta lashe kofin bana

Shugaban kulob, Florentino Perez, zai bayyana tare da ‘dan wasan da ya lashe gasar cin kofin Duniya da kasar Sifen.”

Sergio Ramos zai bayyana ta kafar yanar gizo. Za ayi zaman ne da karfe 12:30 na rana.

Tarihin Sergio Ramos a Madrid

Marca ta ce Sergio Ramos ya zo Madrid ne daga Sevilla a 2005, ya samu damar buga wasanni 671. Bayan ya dade a kungiyar, ya zama mai rike kambun 'yan wasa.

Daga cikin kofin da ‘dan wasan ya ci har da kungiyar Real Madrid akwai La Liga biyar, Copa del Reys biyu, gasar cin kofin Turai biyu da kofin kulob na Duniya hudu.

KU KARANTA: Tsohon Kocin Real, Chelsea, Mourinho zai rike AS Roma

Sergio Ramos
Sergio Ramos mai tsaron baya Hoto: www.skysports.com
Asali: UGC

A lokacin da yake bugawa Real Madrid ne Ramos ya ci gasar Euro har sau biyu a kasar Sifen. Haka zalika tauraron ya ci kofin kwallon Duniya a shekarar 2010.

Bayan zamansa kyaftin, Ramos mai shekara 35 ya na da kwallaye fiye da 100. Ba kasafai ne aka saba ganin ‘dan wasan baya mai irin wadannan tulin kwallaye ba.

A shekarar bana, Ramos bai buga wasanni da dama ba saboda rashin lafiya. Hakan ya jawo har ya gagara zuwa gasar cin kofin Turai wanda ake yi a kasar Hungary.

Dazu kun samu rahoton yadda Cristiano Ronaldo ya yi sanadiyyar da kamfanin Coca Cola ya yi asara, bayan tsohon ‘Dan wasan na Real Madrid ya ki shan lemun.

Yayin da aka shirya taron 'yan jarida, sai aka ajiye wa Ronaldo da kocin Portugal robobin lemun Coca Cola a gabansu, shi Ronaldo sai ya dauke na sa daga gabansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel