Messi @ 34: Abubuwan da gwarzon ‘Dan wasan Barcelona ya yi da ba a taba yi ba a kwallo

Messi @ 34: Abubuwan da gwarzon ‘Dan wasan Barcelona ya yi da ba a taba yi ba a kwallo

A ranar Alhamis hukumar da ke kula da kwallon kafan Turai, UEFA ta tuna da Lionel Messi a daidai lokacin da yake bikin cika shekaru 34 a Duniya.

UEFA ta jero tarihin da ‘dan wasan na kungiyar Barcelona ya kafa a Duniya. Daga ciki shi ne ya fi kowa yawan kwallaye tun da aka fara buga La-liga.

Lionel Messi ne ‘dan wasa na bakwai a jerin wadanda su ka fi yawan wasanni a gasar La-liga.

Ga wasu daga cikin inda Lionel Messi ya ciri tuta

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta ba Mikel Obi mukami

Tarihin da Messi ya kafa a kwallo

1. A ‘yan wasan da su ka zo Sifen daga waje, babu wanda ya buga wasannin da Lionel Messi ya buga a La-liga: 520

2. Kwallayen da ba a taba ci ba a shekara guda, a Sifen (2011): 50

3. Yawan kwallayen da Lionel Messi ya ci wa Barcelona a La-liga: 474

4. Yawan kwallaye a wasanni rukunin farko na gasar kofin Turai: 71

5. Yawan kwallaye a wasanni rukuni na biyu na gasar kofin Turai: 28

6. Yawan Ballon d'Or: 6

7. Yawan zura kwallaye uku a wasa guda: 36

8. Yawan kwallaye a shekara (Kasa da kulob a 2012): 79

9. Yawan la-liga (ga wanda ba ‘dan Sifen ba): 10

10. Yawan kyautar takalmin turai: 6

11. Yawan kofi a kulob: 35

Lionel Mess
Lionel Messi a Barcelona Hoto: www.thetimes.co.uk
Asali: UGC

KU KARANTA: Carlo Ancelotti ya dawo Real Madrid

Ba a nan kadai Messi ya tsaya ba:

12. Shi ne ke bin Cristiano Ronaldo a yawan kwallaye a gasar kofin Turai: 123

13. Na biyu a yawan kwallaye wasannin Turai: 120

14. Wanda ya fi kowa ci wa kasar Argentina kwallo: 73

15. ‘Dan autan wanda ya ci kwallo a kofin Duniya: Shekara 18 da kwanaki 357

Kwanakin baya kun ji cewa Cristiano Ronaldo ya yi sanadiyyar da kamfanin Coca Cola ta tafka asarar makudan kudi yayin da ake buga gasar Euro na turai.

Jagoran ‘yan wasan na Portugal ya ture lemun Coca Cola da aka ajiye masa. Wannan ya sa hannun jarin kamfanin ya ragu da 1.6% a cikin ‘yan sa’o’i kadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel