'Yan sanda sun kama dilan ESN/IPOB na miyagun kwayoyi, an samu kwayoyin N150m

'Yan sanda sun kama dilan ESN/IPOB na miyagun kwayoyi, an samu kwayoyin N150m

  • Rundunar 'yan sandan jihar Imo ta kama dilan miyagun kwayoyi a jihar Imo
  • An kama shi da miyagun kwayoyin da zasu kai darajar kudi har N150 miliyan
  • Ya tabbatar da cewa shi ke rarraba kwayoyi ga 'yan ESN da IPOB a yankin

Owerri, Imo

'Yan sandan jihar Imo sun damke wani dilan miyagun kwayoyi wanda aka tabbatar yana samarwa masu son raba kasar da sauran kungiyoyin ta'addanci a jihar.

'Yan sandan sun ce sun kwace kwayoyi wadanda darajarsu ta kai N150 miliyan, Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya ce wannan cigaban ya faru ne sakamakon bayanan sirri, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: An kuma: Bidiyon Zukekiyar Baturiya da ta Dira a Najeriya Domin Masoyinta ya bazu

'Yan sanda sun kama dilan ESN/IPOB na miyagun kwayoyi, an samu kwayoyin N150m
'Yan sanda sun kama dilan ESN/IPOB na miyagun kwayoyi, an samu kwayoyin N150m. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno

Bayanin ya kai ga kamen wani Obinna Ohaji, 28, wanda ya yi basaja a matsayin direba mai neman fasinjoji a wata bas kirar Nissan da rubutun "ENDLESS GOD" da lamba ABUJA KUJ 88 XC tare da wani Samuel Egwi mai shekaru 36 kusa da tashar motar Owerri, jihar Imo.

Kara karanta wannan

Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno

"Bayan duba bas din, an samu wani abu fari mai yawa wanda ake zargin hodar Iblis ce kuma an boyeta a tsanake a bas din.

“Bayan tuhumarsa, direban bas din yace abun fari da aka gani wata budurwa mai suna Elele ta bashi ya kai jihar Ribas.

“A tsanake ya jagoranci rundunar zuwa iyakar jihohin Imo da Ribas inda aka samu wani Samuel mai shekaru 17 wanda zai karba kuma aka kama shi.

“Ya sanar da cewa shi ke samarwa kungiyoyin ta'addanci na Ribas kwayoyi. Ya jagoranci rundunar zuwa gidan wani dila a Umuaka dake karamar hukumar Njaba mai suna Nnamuka Uchenna mai shekaru 32, wanda aka kama.

“Bayan duba farfajiyar gidan, an sake samun farin abun kuma an gano cewa auna shi ake yi domin siyarwa.

"An kama wani Chinedu Ukaegbulam mai shekaru 20 da Augustine Ete, mai shekaru 39.

“An gano cewa sune ke rarrabe miyagun kwayoyi ga dukkan sansanin ta'addanci na jihar."

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

A wani labari na daban, wani dan gidan sarautar Kajuru da ya bukaci a boye sunansa ya bada labarin gamonsu da 'yan bindigan da suka sace mahaifinsu, Alhaji Alhassan Adamu, Sarkin Kajuru a ranar Lahadi.

Daily Trust ta ruwaito yadda miyagun 'yan bindiga suka yi awon gaba da sarkin tare da wasu 13 daga cikin iyalansa bayan sun kutsa gidansa a ranar Lahadi.

Amma kuma an sako shi a ranar Litinin yayin da 'yan bindigan suka bar sauran a hannunsu. Majiyar wacce take daga cikin tawagar da taje karbo sarkin, ta ce 'yan bindgan sun kira su ta wayar sarkin bayan sallar la'asar kuma sun ce su shirya karbarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel