Hatsarin motocci ya yi sanadin salwantar rayyuka 9 a Yobe

Hatsarin motocci ya yi sanadin salwantar rayyuka 9 a Yobe

  • Hatsarin mota biyu sun hallaka rayyukan mutane tara a jihar Yobe
  • Hukumar kiyayye haddura na FRSC ta tabbatar da afkuwar haduran
  • FRSC ta ce gudu fiye da kima da daukan kaya da yafi karfin motoccin ya janyo hatsarin

Mutane tara sun riga mu gidan gaskiya, wasu da dama sun jikkata sakamakon hatsarin mota biyu da suka faru a jihar Yobe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hatsarin na farko wanda ya faru a ranar Talata, ya afku ne tsakanin wata mota kirar Toyota Hummer bus mai rajista BAM 285XA a kan hanyar Bauchi zuwa Potiskum.

DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Hatsarin motocci ya yi sanadin salwantar rayyuka 9 a Yobe
Jami'in hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC. Hoto: Vangaurd
Asali: UGC

Mutum uku suka rasu a hatsarin yayin da wasu ukun suka samu rauni.

A cewar Daily Trust, hatsarin mota na biyun kuma ya ritsa da wata Toyota Bus mai lamba KJA 12 XA, a ranar Laraba a Garin Alhaji da ka hanyar Potiskum zuwa Kukuri.

Kara karanta wannan

Fashola: Ba mu da matsalar ƙaranci gidaje a Nigeria, akwai gidaje masu yawa da babu mutane a ciki

Mutane shida ne suka rasa rayyukansu yayin da wasu mutane 13 suka samu mabanbantan rauni.

FRSC ta tabbatar da hadduran biyu

Hukumar kiyaye haddura na kasa, FRSC, reshen jihar Yobe, a ranar Laraba ta tabbatar da afkuwar hadduran biyu.

KU KARANTA: Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Hussaini Haruna, jami'in wayar da kan jama'a na hukumar, ya ce fashewar taya da gudu fiye da ka'ida da daukan kaya da ya fi karfin motoccin ne suka yi sanadin hatsarin.

Ya ce an kwashe gawarwakin wadanda suka rasu sannan an kai wadanda suka yi rauni babban asibitin Potiskum.

Ya bukaci masu motocci su rika tuki bisa ka'idojin da hukumar ta bayar.

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

A wani labarin mai kama da wannan, Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mata tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

'Yan uwa 3 sun sheka barzahu bayan sun kwashi garar Amala a Ilorin

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel