Bikin babban Sallah: Masarautar Daura ta bayyana matsayarta a kan Hawan Sallah

Bikin babban Sallah: Masarautar Daura ta bayyana matsayarta a kan Hawan Sallah

  • Sarkin Katsina, Mai martaba Umar Faruq Umar ya kashe Hawa yayin bikin babban sallah mai zuwa
  • Danejin Daura, Abdulmumin Salihu ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar
  • Ya bayyana matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a matsayin dalilin soke Hawan Sallan

Masarautar Daura da ke Jihar Katsina ta bayyana cewa an dakatar da Hawan Sallah a bikin Babbar Sallah da za a yi saboda matsalar rashin tsaro da ake fama da shi.

A cikin wata sanarwa da Danejin Daura, Abdulmumini Salihu ya fitar ranar Talata, 13 ga watan Yuli, ya ce Mai martaba Sarki Umar Faruq Umar ya ɗauki matakin ne saboda matsalolin tsaro da suka addabi yankin masarautar, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta

Bikin babban Sallah: Masarautar Daura ta bayyana matsayarta a kan Hawan Sallah
Masarautar Daura ta soke Hawan babban Sallah saboda rashin tsaro Hoto: Galaxy Television
Asali: UGC

Sanarwar ta ce:

"A maimakon haka, za a gudanar da Sallar Idi kamar yadda aka saba, bayan an kammala za a gudanar da addu'o'i na musamman a fadar mai martaba sarki don neman dawwamammen zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

A ranar 20 ga watan Yuli wanda ya yi daidai da ranar 10 ga watan Zul Hijja na shekarar Hijira ta 1442 ne daukacin Al’umman Musulmi za su gudanar da bikin Babbar Sallah.

Garin Daura wanda shi ne mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, na fama da hare-haren 'yan bindiga waɗanda ke sace mutane da kashe su don neman kuɗin fansa.

KU KARANTA KUMA: Luguden wuta: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 120 a dajin Sububu dake Zamfara

Masarautar Katsina: Abin da ya sa mu ka dakatar da bikin hawan Sallah a bana

Idan za ku tuna, a lokacin karamar Sallah ma Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabiru Usman CFR, ya bada sanarwar hana gudanar da bukukuwan hawan sallah.

Abdulmumin Kabiru Usman ya sanar da daukacin mutanen Katsina cewa matsalar sace-sace da kashe-kashen da ake yi ya sa aka dauki wannan matakin.

Sarkin ya bayyana cewa shawarwarin da ya samu daga gwamnati, jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya suka sa aka yi watsi da shagulgulan karamar sallah.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Buhari ya shirya liyafar cin abincin dare tare da sanatoci 109 a yau Talata

Asali: Legit.ng

Online view pixel