Zamfara: Luguden bama-baman NAF ya aika mata da 'ya'yanta 4 barzahu a Sububu

Zamfara: Luguden bama-baman NAF ya aika mata da 'ya'yanta 4 barzahu a Sububu

  • Ruwan bama-baman sojin saman Najeriya ya janyo mutuwar mata da 'ya'yanta hudu
  • A ranar Litinin ne sojin saman suka ragargaji sansanin 'yan bindiga dake dajin Sububu a Zamfara
  • An gano cewa sojojin sun yi kuskure inda suka yi wa kauyen Sububu luguden bama-bamai a Zamfara

Sububu, Zamfara

Luguden wutan da jiragen yakin sojin saman Najeriya suka yi wa 'yan bindiga ya hada da ran wata mata tare da 'ya'yanta hudu a Sububu dake jihar Zamfara.

Majiyoyi daban-daban sun sanar da Daily Trust cewa jiragen yakin NAF sun tsinkayi dajin Sububu tsakanin kananan hukumomin Shinkafi da Maradun yayin da mugun lamarin ya faru.

KU KARANTA: Yariman Kajuru ya bayyana abinda 'yan bindiga suka sanar masa kafin sakin mahaifinsa

Zamfara: Luguden bama-baman NAF ya aika mata da 'ya'yanta 4 barzahu a Sububu
Zamfara: Luguden bama-baman NAF ya aika mata da 'ya'yanta 4 barzahu a Sububu. Hoto daga @vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Sunaye: Gimbiya da dan shekara 1 daga cikin iyalin sarkin Kajuru dake hannun 'yan bindiga

Dajin Sububu shine yanzu babbar maboyar 'yan bindiga a jihar Zamfara. Daga dajin suke kaddamar da hari kan matafiya a babban titin Sokoto zuwa Gusau da kuma kauyukan jihohin Sokoto da Zamfara.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 120 a dajin Sububu dake Zamfara

Majiyoyin sun ce an kai samamen ta jiragen yakin wurin karfe 2 na ranar Litinin.

A hirar waya da aka yi da mutane hudu, sun tabbatarwa Daily Trust cewa jiragen yakin sun yi kuskure inda suka dinga sakin bama-bamai a kauyen Sububu a maimakon maboyar 'yan bindigan.

"Bama-baman sun halaka mata da 'ya'yanta hudu. Yara biyu daga ciki duk matasa ne. Akwai wata tsohuwa da ta samu miyagun raunika sakamakon farmakin," wani mazaunin Sububu ya tabbatar.

Ya ce hatta sabon masallacin Juma'a da gagarumin dan bindiga Halilu Sububu ya gina sai da aka tarwatsa shi.

Majiyar ta ce babu kowa a ciki masallacin saboda harin ya faru ne bayan jama'a sun kammala sallar azahar.

A wani labari na daban, majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da Lauretta Onochie, tsohuwar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun gano rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan tsohuwar hadimarsa Lauretta Onochie a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta daga jihar Delta.

An yi watsi da sunan Onochie ne bayan duba rahoton kwamitin hukumar zabe mai zaman kanta na majalisar dattawa wanda yake samun shugabancin Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng