Cikakken Bayani: NAFDAC Ta Amince da Sabbin Rigakafin COVID19, Ta Faɗi Amfani da Hatsarinsu
- Hukumar NAFDAC ta amince da sabbin allurar rigakafin cutar COVID19 guda biyu
- Shugaban hukumar, Farfesa Moyi Adeyeye, ita ce ta bayyana haka ranar Laraba a Abuja
- Ta bayyana sunan rigakafin da, Moderna da Sputnik, tace suna da amfani kuma akwai haɗari
Hukumar dake kula da ingancin magunguna da abinci, NAFDAC, ta amince da ƙarin rigakafin cutar COVID19 guda biyu da za'a yi amfani da su a Najeriya, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar da Wani Muhimmin Aiki Na Biliyoyin Naira Bayan Shekara 40 da Fara Shi
Rigakafin da hukumar ta amince da su sune, Moderna da Sputnik, kuma dukkan sunan amince da su wajen buƙatar gaggawa, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Darakta janar na hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ita ce ta sanar da haka a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Adeyeye ta bayyana cewa duk da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ba ta amince da rigakafin Sputnik ba, amma NAFDAC ta gudanar da bincike na musamman a kan rigakafin kuma an gano cewa amfaninta ya fi hatsarin yawa.
Kwana 15 muna bincike
Adeyeye tace kwamitin rigakafi na hukumar NAFDAC yana kula da dukkan rigakafin cutar duk kuwa da cewa suna da ingancin amincewa daga wasu ƙasashe da kuma amincewar gaggawa na hukumar lafiya ta duniya WHO-EUL.
Tace duk wata rigakafin COVID19 da ta samu amincewar ɗaya daga cikin waɗancan biyun to tana da inganci da aminci.
KARANTA ANAN: EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya
Wani sashin jawabinta, tace:
"Hukumar NAFDAC ta shafe kwanaki 15 wajen binciken rigakafin domin tabbatar da amfaninsu ya fi hatsarin su nesa ba kusa ba, da kuma tabbatar da an sanya ido a kan duk wata matsala da yin rigakafin ka iya haifarwa."
A wani labarin kuma Bayan Kin Amincewa da Farko, Sanatoci Sun Amince da Naɗin Wani Kwamishinan Zaɓe INEC
Bayan sun ƙi amincewa ranar Talata, Sanatoci sun amice da naɗin farfesa Adam a matsayin kwamishinan Zaɓe.
Wannan ya biyo bayan nazari da sanatocin suka yi kan rahoton kwamitinta dake kula da al'amuran INEC.
Asali: Legit.ng