Tinubu ya inganta dakin karatun Arewa House a Kaduna, yayin da Sanwo-Olu ya yaba masa

Tinubu ya inganta dakin karatun Arewa House a Kaduna, yayin da Sanwo-Olu ya yaba masa

  • Jagoran Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ya inganta dakin karatu na Arewa house
  • Da yake jawabi a wajen taron, Babajide Sanwo-Olu ya yaba wa dakin karatun na Arewa House sakamakon kula da shi
  • Haka nan, gwamnan na Legas ya bayyana fatan cewa dakin karatun zai ci gaba da kasancewa mai mahimmanci a Arewacin Najeriya

Tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya yada angizonsa zuwa Arewacin kasar.

Wannan karon, tsohon Gwamnan kana mai fatan takarar shugaban kasa a 2023 inganta dakin karatu na Arewa House ya yi.

Karamcin na Tinubu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin Legas ta aike wa kafar Legit.ng.

Wadanda suka kasance a bukin kaddamar da inganta dakin karatun na Arewa a Jihar Kaduna sun hada da Gwamna Babajide Sanwo-Olu, wanda mataimakinsa, Dokta Kadri Obafemi Hamzat ya wakilta.

Kara karanta wannan

Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu

Da yake jawabi a wajen taron, gwamnan ya ce abin farin ciki ne ganin cewa cibiyar ta samar da takardu na tarihi da al'adun mutane.

Sakamakon haka ne gwamnan ya yaba wa jagoran jam'iyyar na kasa saboda ganin bukatar inganta dakin karatun na Arewa House tare da yin alkawarin bayar da kudadensa da dukiyoyinsa wajen inganta dakin karatun yayin taron lakcan shekara-shekara na tunawa da Arewa House na 11.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

Tinubu ya inganta dakin karatun Arewa House a Kaduna, yayin da Sanwo-Olu ya yaba masa
Tinubu ya inganta dakin karatun Arewa House a Kaduna Hoto: Tinubu
Asali: Twitter

DUBA NAN: Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka

Wani rahoto ya nuna cewa akwai rashin jituwan da yake karuwa a cikin jam'iyyar APC reshen Jihar Legas.

A cewar rahoton, Gimbiya Aderenle Adeniran Ogunsanya, tsohuwar sakatariyar gwamnatin jihar tare da Abdul Azzez Adediran, wanda ya shirya taron Lagos4Lagos sun hada hancin mambobin jam’iyyar sama da 6,000 domin kalubalantar shugabancin siyasar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Adediran da Ogunsanya sun yi kira ga kwamitin riko na Gwamna Mai Mala-Buni da ya kori kwamitin rikon na Legas da Cif Tunde Balogun ke shugabanta.

Jagoran Ibo a Legas ya yi hasashen abun da zai faru idan Tinubu ya zama shugaban Najeriya

Joe Igbokwe, mai ba gwamnan jihar Legas shawara na musamman kan magudanan ruwa da albarkatun ruwa, ya ce "abubuwa zasu inganta" idan Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban Najeriya.

Igbokwe, jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, ya fadi hakan ne yayin amsa tambayoyi a wata hira da ya yi da BBC Pidgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel