Yanzu-Yanzu: Uwar jam'iyya ta dakatad da Rochas Okorocha daga APC

Yanzu-Yanzu: Uwar jam'iyya ta dakatad da Rochas Okorocha daga APC

Kwamitin gudanarwan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dakatad da tsohon gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha, kan laifin yiwa jam'iyyar zagon kasa.

Sanarwan dakatad da Okorocha na kunshe cikin a wasikar da aka aike ranar 12 ga Yuli, 2021, dauke da sanya hannun shugaban jam'iyyar Mai Mala Buni da kuma Sakataren jam'iyyar John Akpanudoedehe.

A cewar wasikar, an yanke shawarar dakatad da Okorocha ne saboda zagon kasan da yake yiwa jam'iyyar, rahoton TheCable.

Wai sashen wasikar yace:

"Muna sanar da kai cewa kwamitin gudanarwan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabbatar da dakatar da kai da akayia matakin jihar Imo kan laifin yiwa jam'iyyarmu zagon kasa."

DUBA NAN: Yadda zamu ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Osinbajo

Yanzu-Yanzu: Umar jam'iyya ta dakatad da Rochas Okorocha daga APC
Yanzu-Yanzu: Umar jam'iyya ta dakatad da Rochas Okorocha daga APC
Asali: Original

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Gwamnatin Imo Ta Rufe Makarantar Rochas Okorocha a Owerr

Gwamnatin Jihar Imo, a ranar Talata ta rufe makarantar tsohon gwamna Rochas Okorocha mai suna Rochas Foundation College da ke Orji, a Owerri babban birnin jihar, The Punch ta ruwaito.

Jami'an gwamnati sun isa wurin da makarantar ya ke, wacce tsohon gidajen ma'aikatan gidan rediyon jihar Imo ne sannan suka rufe wurin.

Wakilin The Punch, wanda ya ziyarci wurin ya ga babban ginin da a yanzu gwamnatin jihar ta amshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel