Yariman Kajuru ya bayyana abinda 'yan bindiga suka sanar masa kafin sakin mahaifinsa

Yariman Kajuru ya bayyana abinda 'yan bindiga suka sanar masa kafin sakin mahaifinsa

  • Wani yarima a masarautar Kajuru ya bada labarin yadda aka karbo Sarki Alhassan Adamu daga wurin 'yan bindiga
  • Kamar yadda ya sanar, 'yan bindigan sun kira inda suka ce a aje a karba sarkin bayan sallar la'asar a ranar Litinin
  • Yace 'yan bindigan sun dinga bada hakuri kan sace sarkin da suka yi kuma sun ce natsuwa ta kaurace musu tun bayan daukeshi da suka yi

Kajuru, Kaduna

Wani dan gidan sarautar Kajuru da ya bukaci a boye sunansa ya bada labarin gamonsu da 'yan bindigan da suka sace mahaifinsu, Alhaji Alhassan Adamu, Sarkin Kajuru a ranar Lahadi.

Daily Trust ta ruwaito yadda miyagun 'yan bindiga suka yi awon gaba da sarkin tare da wasu 13 daga cikin iyalansa bayan sun kutsa gidansa a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin iyalin Yar'adua da Mijin tsohuwar matar Danbaba Suntai

Yariman Kajuru ya bayyana abinda 'yan bindiga suka sanar masa kafin sakin mahaifinsa
Yariman Kajuru ya bayyana abinda 'yan bindiga suka sanar masa kafin sakin mahaifinsa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon Ahmed Musa tare da dalleliyar sabuwar amaryarsa sun bayyana

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa

Amma kuma an sako shi a ranar Litinin yayin da 'yan bindigan suka bar sauran a hannunsu.

Majiyar wacce take daga cikin tawagar da taje karbo sarkin, ta ce 'yan bindgan sun kira su ta wayar sarkin bayan sallar la'asar kuma sun ce su shirya karbarsa.

Yace bayan isarsu wurin kusa da yankin Gengere, 'yan bindiga uku dauke da makamai sanye da kayan sojoji sun bada hakuri tare da neman yafiya kan sace sarkin da suka yi.

"Mun kasa yadda. Mun tsaya muna kallonsu yayin da suke bada hakuri. Sun ce sun kasa samun natsuwa tunda suka sace shi. Sun ce mu tafi da shi yayin da za a cigaba da ciniki kan sakin sauran a ranar Talata," yace.

Daily Trust ta tattaro cewa ba a biya ko sisin kwabo ba kafin 'yan bindigan su saki sarkin mai shekaru tamanin da biyar wanda ya gaji tsohon sarkin Kajuru na 1978.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru

Wurin karfe 5:25 na yammaci ne labarin sako sarkin ya bazu, lamarin da yasa mazauna yankin suka dinga murna tare da tururuwar ganinsa.

Galadiman masarautar Kajuru kuma daya daga cikin 'yan majalisar nadin sarakuna, Dahiru Abubakar, ya tabbatar da dawowar sarkin lafiya cike da koshin lafiya.

A wani labari na daban, bayanai na cigaba da bayyana kan harin da aka kai masarautar Alhaji Alhassan Adamu, Sarkin Kajuru.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun kutsa fadar basaraken inda suka yi awon gaba da shi tare da iyalansa 13.

Garin Kajuru yana da nisan kilomita 37 daga birnin Kaduna. Garin yana nan a babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia kuma yana da iyaka da Chikun ta Kujama inda aka sace dalibai 121 na makarantar Bethel Batist a ranar Litinin da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel