Da duminsa: Majalisa tayi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan INEC
- Majalisar dattawan Najeriya ta yi fatali da sunan Lauretta Onochie a matsayin kwamishinan INEC
- A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabeta
- Sai dai a makon da ya gabata ta bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa domin tantancewa
Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da Lauretta Onochie, tsohuwar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Daily Trust ta ruwaito.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan tsohuwar hadimarsa Lauretta Onochie a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta daga jihar Delta.
KU KARANTA: An kuma: Bidiyon Zukekiyar Baturiya da ta Dira a Najeriya Domin Masoyinta ya bazu
KU KARANTA: Dalla-dalla: Gagarumin Luguden Wuta na Sa'a 1 aka yi Kafin Sace Sarkin Kajuru
An yi watsi da sunan Onochie ne bayan duba rahoton kwamitin hukumar zabe mai zaman kanta na majalisar dattawa wanda yake samun shugabancin Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano.
Majalisar ta kara da dakatar da amincewa da Farfesa Sani Mohammed Adam har sai anyi wani zaman majalisa a gaba.
Kwamitin ya bukaci a yi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta saboda zabenta ya sabawa sashi na 14, sakin layi na 3 nna kundun tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Kwamitin ya ce a halin yanzu akwai kwamishinan hukumar zabe daga jihar Delta, inda Onochie ta fito, Daily Trust ta tabbatar.
Zaben Onochie a matsayin kwamishinan INEC da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ya janyo cece-kuce daban-daban daga jama'a a kasar nan, ballantana jam'iyyar APC ta hammaya.
A wani labari na daban, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya musanta rahoton dake yawo na nada gwamna a wasu yankunan jihar Borno da Boko Haram tare da ISWAP suka yi.
A makon da ya gabata, bidiyon da ake zargin na nada gwamnan Boko Haram a Borno ne ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, Daily Trust ta ruwaito.
Hukumar rikon kwarya ta 'yan ta'addan ta samu shugabancin wani Abba Kaka, wanda aka nada a matsayin shugaban wasu yankunan Borno.
Asali: Legit.ng